Shugaban ƙaramar hukumar Zaki ya yaba da ayyukan ci gaban Gwamna Bala Muhammad

Spread the love

Daga GAMBO ISA

Shugaban ƙaramar hukumar Zaki, Dakta Adamu Yakubu Sakwa, ya yabawa Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammad, bisa irin gagarumar gudunmawar da yake bayarwa wajen bunƙasa ci gaba da kyautata rayuwar al’ummar jihar. A cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, Sakwa ya bayyana cewa gwamnatin Bala Muhammad ta samu nasarori masu yawa a fannoni daban-daban da suka haɗa da ilimi, lafiya, noma, tsaro da samar da ababen more rayuwa.

Ya ce daga cikin manyan ayyukan da gwamnatin ta aiwatar akwai gina da gyaran sakatariyoyin gwamnati na zamani, samar da fitilun hasken rana a yankuna daban-daban, da kuma gina hanyoyin cikin gari da na haɗa al’ummomi. Haka kuma ya yabawa gwamnatin bisa gina kasuwanni da shaguna na zamani a Zaki tare da samar da ingantattun ofisoshi da ɗakunan taro masu amfani da hasken rana.

Dakta Sakwa ya bayyana cewa gwamnatin Bala Muhammad ta aiwatar da sama da ayyukan raya ƙasa 228 a Zaki da sauran ƙananan hukumomin jihar.

Ya ce daga cikin waɗannan ayyuka akwai gina hanyoyin Trunk B da suka haɗa yankin Sakwa, waɗanda ya ce ba a samu irin su ba tun zamanin gwamnatin Shehu Shagari a shekarun 1980.

A fannin tsaro da lafiya kuwa, shugaban ƙaramar hukumar ya yabawa gwamnan kan gina ofisoshin ‘yan sanda, tallafa wa jami’an tsaro da ƙungiyoyin sintiri, da samar da motocin aiki. Haka kuma ya jinjina masa kan gina asibitin zamani a Zaki, inganta cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko, horar da ma’aikatan lafiya da samar musu da kayan aiki domin inganta ayyukan kula da lafiyar jama’a.

Dangane da noma da bunƙasa matasa, Dakta Sakwa ya buƙaci manoma da makiyaya su ci gaba da amfani da shirye-shiryen tallafin noma da kiwo na gwamnatin jihar. Ya kuma yabawa shirye-shiryen horas da matasa sana’o’i da kafa cibiyar masana’antar GSM Industrial Hub Village, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arziki.

Ya kammala da kira ga al’umma da ma’aikatan gwamnati da su mara wa shirye-shiryen gwamnati baya tare da ci gaba da addu’ar zaman lafiya da ci gaban Jihar Bauchi da Najeriya baki ɗaya.

By ukarofi