Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina tasha alwashin cigaba da haɗa hannu da masu ruwa da tsaki a harkar wasanni domin bai wa matasan Jihar Katsina damar ganin sun cimma burin su na buga ƙwallon ƙafa a ƙasashen waje.
Mataimakin gwamnan Jihar Katsina Malam Faruq Lawal Joɓe ya bayyana haka a lokacin da ya amshi baƙuncin tawagar wakilan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta FC Torpedo Belaz Zhodino da ke ƙasar Belarus waɗanda suka zo Jihar domin gudanar da shirin baje kolin ‘yan wasan ƙwallon ƙafa da Katsina football academy ta ɗauki nauyi.
‘Yan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta FC Torpedo daga ƙasar Belarus sun ziyarci mataimakin gwamnan Jihar Katsina domin gaisuwa da gabatar da kansu.
Wakilan ƙungiyar sun zo Jihar Katsina ne ta hannun makarantar koyar da ƙwallon ƙafa ta jihar Katsina domin zaɓen matasa masu ƙwarewa a harkar taka tamola, da nufin taimaka masu wajen cimma burinsu na harkar ƙwallo.
Wakilan ƙungiyar tare da jagorancin daraktan makarantar koyar da ƙwallo ta Jihar Katsina (Katsina State Football Academy), sun gana da mataimakin gwamnan Katsina a ofishinsa da ke tsohon gidan gwamnati.
A yayin jawabin sa, Shamsuddeen Ibrahim, daraktan makarantar koyar da ƙwallon kafa ta jihar Katsina, ya ce wakilan sun zo daga ƙasar Belarus domin gano haziƙan matasa masu ƙwarewa a wasan ƙwallon ƙafa, inda za su gudanar da aikin zaɓen cikin kwanaki huɗu.
Shi ma a nasa jawabin Vladimir Bahdanau, ɗaya daga cikin wakilan ƙungiyar FC Torpedo ya bayyana wa mataimakn gwamnan cewa sun zo jihar ne domin gano matasa da suka ƙware a harkar ƙwallo domin ba su damar shiga manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na duniya.
A nasa ɓangaren, Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Faruq Joɓe, ya bayyana godiyarsa bisa ziyarar girmamawar da suka kawo masa. Ya ƙara da cewa Katsina State Football Academy makaranta ce da ke tafiya daidai da manufofin gwamnati wajen gina makomar matasa musamman a ɓangaren ƙwallon ƙafa.
Haka kuma ya bayyana cewa gwamnatin jihar a shirye take ta tallafa wa duk masu kawo irin wannan cigaba a Jihar Katsina.
