Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana cewa hana gudanar da hawan Sallah a Kano na da matuƙar illa ga tattalin arzikin jihar, yana mai cewa bikin na taka muhimmiyar rawa wajen jawo masu yawon buɗe ido da bunƙasa harkokin kasuwanci.
Sarkin ya bayyana hakan ne yayin da yake karɓar baƙuncin shugaban gukumar kula da yawon vuɗe Ido ta ƙasa a fadarsa da ke Ƙofar Kudu.
Ya ce hawan Sallah da hawan daba ba al’amura ne na al’ada kawai ba, har ila yau suna taimakawa wajen samar da kuɗaɗen shiga ga dubban mutane da suka haɗa da ƴan kasuwa, masu sana’o’in hannu, masu otal-otal da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin yawon buɗe ido.
Muhammadu Sanusi II ya jaddada cewa duk wani mataki da zai hana gudanar da bukukuwan hawan Sallah yana da tasiri kai tsaye ga tattalin arzikin Kano, kasancewar jihar na daga cikin manyan cibiyoyin al’adu da yawon buɗe ido a Najeriya.
Kazalika, sarkin ya kuma yi kira da a cire siyasa daga lamurran da suka shafi bukukuwan gargajiya, yana mai cewa kiyaye al’adu da martabar masarautu na da muhimmanci wajen bunƙasa haɗin kai da ci gaban al’umma.
Sannan ya yabawa ƙoƙarin gwamnatin tarayya na farfaɗo da harkokin yawon buɗe ido a ƙasar nan, tare da buƙatar a ƙara mai da hankali kan gyaran wuraren tarihi da na yawon buɗe ido a Kano domin ƙarfafa tattalin arzikin jihar.
