
Shugaba Bola Tinubu zai gabatar da jawabi a zaman haɗin-gwiwar na Majalisar Dokoki ta Ƙasa a ranar 12 ga watan Yuni, a wani ɓangare na bukukuwan cika shekaru 27 da dawo da mulkin dimukraɗiyya a Nijeriya.
Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume ne ya faɗi hakan yayin ƙaddamar da kwamitin ministoci da aka ɗora wa alhakin shirya bukukuwan a Abuja, inda ya a ce jawabin shugaban ƙasar zai kasance ɗaya daga cikin manyan abubuwan da za su gudana a ranar.
Ya bayyana cewa Ranar Dimukraɗiyya wata dama ce ta tunawa da sadaukarwar waɗanda suka yi gwagwarmayar dawo da mulkin dimukraɗiyya musamman marigayi Moshood K. Abiola da sauran jaruman gwagwarmayar 12 ga Yunin shekarar 1993.
A cewarsa, gwamnatin tarayya za ta yi amfani da bikin wajen nuna nasarorin da ta samu wajen ƙarfafa cibiyoyin dimokuraɗiyya da bunƙasa ci gaban ƙasa duk da ƙalubalen tattalin arziki.
Daga cikin shirye-shiryen bikin akwai taron manema labarai na duniya a ranar 4 ga Yuni, addu’ar Juma’a ta musamman a ranar 5 ga Yuni, ibadar coci ta haɗin mabiya addinai a ranar 7 ga Yuni, da kuma lacca ta ranar a ranar 9 ga Yuni.
Haka kuma za a gudanar da shirye-shirye na matasa da mata a ranar 10 ga Yuni. A 12 ga Yuni, shugaban zai yi jawabi ga al’umma, sannan za a kammala bukukuwan da liyafa a lokacin maraice ta ranar.
