
A bayan ƙaddamar da jiga-jigan ‘yan takarar wakilan al’umma ƙarƙashin tutar Jam’yyar APC a Ƙaramar Hukumar Bichi da ke Jihar Kano, Shugabar Matan Jam’iyyar APCn ta yankin, Hajiya Rahana Idris ta jaddada alƙibla da ɗaukacin matan yankin suka dosa a zaɓe mai zuwa na shekarar 2027.
Jami’ar Yaɗa Labarai ta yankin, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo, ta rawaito, Shugabar matan, ta ƙarfafa aniyarsu ta hanyar ci gaba da bada haɗin kai da goyon bayan dukkan ‘yan takarar jam’iyyar tasu na yankin, domin cigaba da inganta rayuwar al’ummar garin Bichi ta fanni lafiya, ilimi, sana’a da kuma ayyukan raya ƙasa domin haɓaka tattalin arzikinsu da kuma bunƙasa garinsu a matakin da suke kai.
“Kin san a duniya ita mace indai za ka tallafi ɗanta ka gama mata komai; mu ko daga biyan kuɗin makarantar nan kamar yadda ya taimaki ɗan Maikaras da ɗan Maiyalo. Wasu ba su da ko naira biyar a gidansu, amma ɗansu har digiri da mastas ya yi ta hanyar Ɗanmajalisar Tarayya. Don haka a Jam’iyyar APC; daga kan Shugaban ƙasa har zuwa zaɓuɓɓukan ƙarshe in Allah ya yarda Ƙaramar Hukumar Bichi za mu ba da ƙuri’a ta ban mamaki!.” Hajiya Rahana Idris Bichi.
A bisa haka ta gode wa dukkan jagororin yankin, musamman Ɗanmajalisar Tarayya mai Wakiltar Bichi, Alhaji Abubakar Kabir Abubakar, dangane da ɗimbun ayyukan alheri na gina rayuwar al’umma kodayaushe. Ta yi fatan da yardar Allah jam’iyyar tasu za ta samu goyon bayan mata ɗari bisa ɗari a garin na Bichi.
“Akwai kuma tsari na mata da shi mai girma Ɗanmajalisar Tarayya na Ƙaramar Hukumar Bichi, Injiniya Abubakar Kabir Bichi wanda ake cewa Abban alheri! Zai zo a yi wa mata na alheri, maganar mata da kike yi dama ana yi mana, ba abin da ba mu raba ba a Karamar Hukumar Bichi; mun raba kuɗi da keken ɗinki da injin markaɗe, da kiwon kifi da kaji, yanzu ma kuma muna nan za mu zo mu yi da izinin Allah.” Hajiya Rahana Idris Bichi.
A ɓangaren mai ɗakin Ɗanmajalisar Tarayyar, Barista Maryam Abubakar Kabir Abubakar, ta yi matuƙar godiya ga alummar Bichi sakamakon bai wa maigidanta damar da zai ci gaba da faɗaɗa ayyukan alheri a sassan yankin da jiha da ƙasa baki ɗaya. Ta kuma jaddada a shirye suke wajen ci gaba da tallafa wa al’amuran mata ɗari bisa ɗari.
“Muna addu’a Allah Ubangiji ya ci gaba da sa albarka a cikin hidimar. Yadda yake kishin ƙasar nan da garinsu, Allah ya ƙara dafa masa ya zama gatan shi da jigonsa, waɗanda kuma ake yi tare da su, Allah ya bar zumunci tarayya ta ci gaba da tafiya har Allah ya kawo babban rabo.” Hajiya Barista Maryam Abubakar Kabir Abubakar Bichi.
