
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Jihar Zamfara ta shirya tallafa wa sama da mata miliyan guda, ‘yan mata da sauran masu ƙaramin ƙarfi a faɗin jihar.
Wannan wani ɓangare ne na shirinta na tallafa wa mata na WEE da nufin inganta lamuran rayukansu na yau da kullum.
Kwamishinar Harkokin Mata ta jihar, Dakta Aisha M.Z. Anka ta bayyana hakan a yayin wani taron ƙara wa juna sani na kwana uku akan shirin Inganta Rayuwar Mata a Gida na Ƙasa a Jihar Zamfara, wanda aka gudanar a Karma Guest Inn, Sakkwato, ranar Talata.
Dakta Aisha, wadda ta samu wakilcin Alhaji Garba Aliyu Gayari, babban Sakataren ma’aikatar, ta ce ciyar da ilimin mata gaba da bayar da kariya da kuma wadata su da kuɗaɗe za su taimaka wajen ƙarfafa zamantakewarsu da kuma ci-gaban yankunansu.
A cewarta, gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ta nuna ƙoƙari akan ci-gaban mata ta tsare-tsare da wasu shirye-shiryen damawa da su a fannonin ilimi, noma, lafiya da jagorancin siyasa.
Ta ƙara da cewa, inganta mata da ‘yan mata na da gagarumar muhimmanci wajen cimma nasarorin ci-gaba a harkar tattali da ci-gaban jihar.
