Nasarawa 2027: Sanata Wadada ya yi kira a yi sulhu bayan nasarar zaɓen fidda gwanin APC

Spread the love

Daga JOHN D WADA a Lafia

Sanata Ahmed Aliyu Wadada mai wakiltar mazaɓar Nasarawa ta Yamma a majalisar dattawa ta tarayya ya amince da zaɓin da magoya bayan jam’iyyar APC suka yi masa a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar a zaɓen 2027 da ke tafe.

Da yake jawabi a wani taron manema labarai a Lafia babban birnin jihar tare da shugabannin jam’iyyar Wadada yace zaɓen fidda gwani na APC din bai samar da “mai nasara ba, kuma babu wanda ya sha kaye” yayi kira da haɗin kai a cikin jam’iyyar.

“Na amince da wannan amanar da ‘yan jam’iyyar mu suka bani a faɗin jihar bisa raɗin kansu a hukumance. Na amince da ita da cikakken alhakin gudanar da aiki da cikakken ƙuduri da gaskiya da niyya da kuma tsayyen ƙuduri na cigaba da yi wa mutanen jihar Nasarawa hidima,” in ji shi.

Ɗan majalisar ya miƙa hannun abota ga sauran ‘yan takara ciki har da Hassan Liman (SAN) da Dr. Fatima Abdullahi da sauran su inda ya yaba ɗaukaka su da sadaukarwar su domin daidaiton jam’iyyar.” Ya kuma buƙaci ‘yan jam’iyyar da suka fusata da sakamakon zaɓen fidda gwanin da waɗanda ke tunanin barin jam’iyyar da su sake tunani yana jaddada cewa “yanzu ne lokacin sulhu da haɗin kai da kuma ɗaukar alhaki tare.”

Wadada ya kuma yaba wa gwamnan jihar na yanzu Abdullahi Sule bisa “jagoranci mai ma’ana” da daidaita yaƙin neman zaɓen sa da shirin sabon fata na shugaba Bola Tinubu inda ya ambaci sauye-sauyen tarayya kan ababen more rayuwa da jari da ƙarfafa cibiyoyi da sauran su.

Da yake bayyana tsarin ci gabansa, dan takarar APC din Sanata Aliyu Wadada ya gabatar da shirin nasa na musamman da ake kira HEARTS a turance wato wani tsari na ginshiƙai shida da ya kunshi:

H-Cigaban Jama’a
E- Inganta Tattalin Arziki
A- Aikin Gona
R- Sauya Karkara
T- Fasaha da Zuba Jari
S- Tsaro

“Burimu abu ne mai sauƙi: tabbatar da cewa kowace al’umma da kowane mai ruwa da tsaki da kowane ɗan kasa ya ji tasirin mulki mai kyau ba tare da la’akari da wuri da matsayin zamantakewa da addini da kabila ko jam’iyya ba” in ji Wadada.

Ya kammala da roƙon masu kaɗa ƙuri’a da su kasance tsintsiya maɗaurinki ɗaya, yana mai cewa: “Tare da haɗin kai a cikin zukatan mu nayi imani ga Allah maɗaukakin Sarki da ƙwarin gwiwa a ƙarfin mu na haɗin gwiwa ina da tabbacin cewa mafi kyawun kwanakin jihar Nasarawa suna gaba.”

By ukarofi

Leave a Reply