‘Yan bindiga sun sace makamai bayan harin ofishin jami’an shige da fice a Oyo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar ‘Yan sanda a Jihar Oyo, ta ce ta fara bincike akan wani kutse da aka yi wa ofishin Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa da ke garin Ogbomoso a daren ranar Talata wayewar Laraba, inda aka yi awon-gaba da makaman jami’an da ke bakin aiki.

Binciken manema labarai ya nuna cewa al’amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:00 na dare a ofishin hukumar da ke kan hanyar Ogbomoso zuwa Ilorin kusa da gidan man NNPC.

Wata majiya ta ce, “Maharan sun farmaki ofishin ne yayin da ake tsaka da gudanar da harkokin aiki a kusa da kasuwar dabbobi ta Ayanyan.”

A cewarta, maharan sun sha ƙarfin jami’an, lamarin da ya sa suka ƙwace makaman da ke hannunsu da ba a tabbatar da adadinsu ba.

An ruwaito cewa, ‘yan ta’addan sun tsere ne jim-kaɗan bayan kai farmakin cikin daren.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta bakin Jami’in hulɗa da jamarta, Olayinka Ayanlade, ta ce ta fara bincike akan al’amarin, wanda binciken farko ya nuna cewa mutane biyar ne suka kai harin.

Ya bayyana cewa, sun tsere da wayar hannun ɗaya daga cikin jami’an, janareta, batirin babur, sannan kuma sun raunata jami’an, waɗanda halin yanzu suna karɓar magani.

By Babaji

Leave a Reply