Daga USMAN KAROFI
Ebola Virus Disease (EVD)cuta ce mai tsanani da ƙwayar cuta ta Ebola ke haifarwa. Tana daga cikin cututtukan da idan aka kamu da ita, mafi yawa ana rasa rai, inda tsakanin kashi 25% zuwa 90% na masu kamuwa da ita kan rasa rayukansu idan ba a gano ta da wuri ba. Masana sun yi imanin cewa jemagu masu cin ‘ya’yan itatuwa (fruit bats) su ne manyan ma’ajiyar wannan ƙwayar cuta.
Yadda Ebola ke yaɗuwa
Ana iya kamuwa da cutar ta hanyar hulɗa da jemagu ko wasu dabbobin da suka kamu da ita kamar birrai, ɓeraye da sauransu. Haka kuma tana yaɗuwa daga mutum zuwa mutum ta hanyar mu’amala da ruwan jiki na mai cutar, kamar:
- Jini
- Amai
- Gudawa
- Yawu
- Gumi
- Hawaye
- Maniyyi
- Nono
Har ila yau, amfani da kayan da suka gurɓata da ruwan jikin mai cutar kamar allurai ko tufafi na iya haddasa kamuwa da ita. Cutar na bayyana a jikin wanda ya kamu daga kwanaki biyu zuwa 21 daga lokacin da ya kamu da ita.
Alamomin Ebola
Alamomin cutar kan fara bayyana ne ba zato ba tsammani, kuma sun haɗa da:
- Zazzabi mai tsanani
- Ciwon kai
- Ciwon tsoka da gaɓoɓi
- Raunin jiki
- Tashin zuciya
- Gudawa
- Ciwon maƙogwaro
A wasu lokuta, marasa lafiya kan samu:
- Jan idanu
- Kuraje a fata
- Matsalar hanta da koda
- Zubar jini daga ciki ko wajen jiki kamar hanci, ido da kunne
Idan ana zargin mutum ya kamu da Ebola, dole ne a ware shi nan take sannan a sanar da hukumomin lafiya. A Nijeriya duk wanda aka samu da irin alamomin cutar a kira hukumar NCDC kan lambar waya 6232 ko kuma asibiti mafi kusa.
Hanyoyin kare kai
- Gujewa hulɗa da ruwan jikin mai cutar.
- Wanke hannu akai-akai da sabulu ko sinadarin kashe ƙwayoyin cuta.
- Gujewa taɓa gawar wanda ake zargin ya mutu da Ebola.
- Kai rahoto ga jami’an lafiya idan an ga alamun cutar.
- Bin ƙa’idojin kariya a filayen jiragen sama da iyakoki.
Waɗannan matakai ne suka taimaka wa Najeriya wajen daƙile ɓarkewar Ebola a shekarar 2014, kuma har yanzu suna daga cikin manyan hanyoyin kariya na duniya.
