Gwamna Raɗɗa ya taya gwamnan Bayelsa, Douye Diri murnar cika shekaru 67 da haihuwa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya aike da saƙon taya murna ga gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, bisa cika shekaru 67 da haihuwa.

Gwamna Raɗɗa ya yaba da nagartaccen jagoranci da kuma gagarumin ci gaban da Gwamna Diri ya samar a Jihar Bayelsa tun bayan hawansa mulki.

Ya bayyana cewa gwamnatin Diri ta nuna cikakken jajircewa wajen inganta rayuwar al’ummar Bayelsa ta hanyar zuba jari a muhimman fannoni da suka haɗa da ilimi, kiwon lafiya, gine-ginen more rayuwa da kuma bunƙasa tattalin arziki.

A cewar Gwamna Raɗɗa: “Mulkin ka ya tabbatar da cewa shugabanci nagari shi ne hidimtawa al’umma da kuma sadaukar da kai wajen tabbatar da ci gaban ƙasa.”

Gwamnan Katsina ya bayyana Gwamna Diri a matsayin shugaba mai hangen nesa, wanda mayar da hankalinsa kan ci gaba mai anfani ga kowa ya sanya Jihar Bayelsa ta zama abin koyi da kuma tushen fata ga al’ummarta.

Haka kuma, ya yaba da yadda gwamnan Bayelsa ke haɗa kai da gwamnatin tarayya da sauran gwamnoni wajen fuskantar ƙalubalen ƙasa da kuma ciyar da ajandar ci gaba gaba.

Gwamna Raɗɗa ya yi addu’ar cewa:

“Allah ya sanya wannan ranar haihuwa ta zo maka da farin ciki da ƙarin ƙarfin gwiwa domin ci gaba da gudanar da ayyukan shugabanci. Allah Ya albarkaci rayuwarka da lafiya, hikima da nasarori a hidimarka ga Bayelsa da Najeriya.”

A matsayinsa na shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewa maso Yamma, Gwamna Raɗɗa ya sake jaddada ƙudirin gwamnonin jihohi na ci gaba da haɗa kai wajen tabbatar da ci gaba da tsaron Najeriya.

Ya kuma yi wa Gwamna Diri da ɗaukacin al’ummar Jihar Bayelsa fatan alheri, wadata da ci gaba mai ɗorewa.

By ukarofi

Leave a Reply