Ƙudirin samar da hukumar daƙile zazzaɓin cizon sauro ya tsallake karatu na uku a Majalisar Dattawa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Majalisar Dattawa ta yi wa ƙudirin dokar neman kafa hukumar yaƙi da cutar zazzaɓin cizon sauro karatu na uku, lamarin da ke nuna ta kammala aikin tantance shi a hukumance.

Za a samar da hukumar ne da nufin kula da bayar da kariya, kulawa da kuma kawo ƙarshen cutar, wadda ake kira da “Malaria” a Nijeriya musamman ganin yadda mutane da dama ke rasa rayukansu sanadiyyar kamuwa da ita a ƙasar.

Sanata Ned Nwoko (Delta ta Arewa) ne ya ɗauki nauyin gabatar da ƙudirin, wanda ya tsallake karatu na uku bayan nazari da kuma karɓar rahoton kwamitin majalisar akan lafiya da Sanata Ipalibo Harry Banigo (Ribas ta Yamma) ya jagoranta.

A cewar kwamitin, hukumar, wadda ake shirin kafawa za ta tsara shirye-shiryen yaƙi da cutar daga yin magani zuwa shafe baki ɗaya a ƙasar.

Haka kuma, hukumar za ta kafa ofisoshin shiyyoyi domin ƙarfafa aiwatarwa ta tsare-tsare akan shari’a, kimiyya da adalci.

By Babaji

Leave a Reply