
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mataimakiyar shugaban Ƙaramar Hukumar Ilejemeje ta Jihar Ekiti, Grace Ogunleye ta shiga matsalar shari’a bayan an tsare ta a gidan gyaran hali na Ado-Ekiti bisa zarge-zargen kitsa makirci da garkuwa da kanta.
Rahotanni sun bayyana cewa an gurfanar da Grace ne a Babbar Kotun Shari’a da ke Ado-Ekiti, babban birnin jihar tare da wasu mutane guda uku a ranar Laraba bayan binciken ‘yan sanda akan al’amarin.
Kotun ta umarci da a tsare mataimakiyar ciyaman ɗin da sauran mutanen a gidan yari har zuwa lokacin da za a sake tayar da batun nasu a gabanta.
Wannan al’amari ya nemi zama wasan kwaikwayo a lamarin da da fari ya sanya damuwa acikin al’umma bayan ruwaito cewa an sace Ogunleye a watan Mayu.
Da yake magana akan al’amarin, Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Sunday Abutu ya ce an gurfanar da waɗanda ake zargin ne bayan gudanar da bincike mai zurfi akan zarge-zargen da ake musu.
A yayin gabatar da hukunci, Alƙali Abayomi Adeosun ya umarci a tsare Grace da abokan nata a gidan yarin Ado-Ekiti.
Sannan, masu binciken sun bayyana cewa, an tsara garkuwar ne domin samar da kuɗaɗen wasu buƙatu da kuma na wasu sabgogin siyasa.
