Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Kwamitin kula da gandun daji (Task Force Committee on Forest Reserve) ya gudanar da taron wayar da kai tare da sauraron ƙorafe-ƙorafen da ƙalubalen da jami’an kula da gandun daji ke fuskanta a Jihar Katsina.
Taron ya gudana ne a sakatariyar ƙaramar hukumar Kankiya inda ya haɗa jami’an kula da gandun daji daga ƙananan hukumomin Kankia, Kusada, Ingawa, Musawa, Matazu, Danmusa, Dutsin-Ma, Kurfi, Safana da Batsari.
Da yake jawabi a wajen taron, shugaban kwamitin, Alhaji Khalil Bako, ya bayyana cewa manufar taron ita ce duba yadda ayyukan kula da gandun daji ke gudana, sauraron ƙalubalen jami’ai da kuma nemo hanyoyin inganta aikin kare muhalli da albarkatun ƙasa.
Ya jaddada muhimmancin bin dokoki da ƙa’idojin da suka shafi kula da gandun daji, tare da bukatar jami’an su kara sanya ido kan sare itatuwa ba bisa ƙa’ida ba da kuma hana mamaye dazukan gwamnati ba tare da izini ba.
Alhaji Khalil Bako ya kuma buƙaci jami’an da su kasance masu gaskiya, riƙon amana da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu, tare da kai rahoton duk wani abu da zai iya zama barazana ga gandun daji da muhalli.
A nasu ɓangaren, jami’an kula da gandun dajin sun gabatar da nasarorin da suka samu da kuma ƙalubalen da suke fuskanta yayin gudanar da aikinsu, tare da yabawa kwamitin bisa samar da wannan dama ta tattaunawa da musayar ra’ayoyi.
Sun kuma bayyana aniyarsu ta ci gaba da haɗa kai da hukumomin gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da kare gandun daji da albarkatun ƙasa domin amfanin al’umma da kuma ɗorewar muhalli.
Taron ya samu halartar mambobin kwamitin da suka haɗa da daraktan survey, mataimakin daraktan forestry, mai bai wa gwamna shawara daga ofishin shugaban fadar gwamnati, wakilan hukumar NSCDC, Rlrundunar ’yan sanda, DSS, ma’aikatan gandun daji da sauran masu ruwa da tsaki.
