Mulki ya fi damun Buhari kan yi wa jama’a aiki – Isyaku Ibrahim

Daga IBRAHIM HAMZA MUHAMMAD

Alhaji Isyaku Ibrahim, dattijo ne mai shekaru 85 a Duniya. Ya kasance ɗan siyasa ne, kuma mai tallafa wa al’umma. Ya yi sharhi dangane da mulkin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, hukumar Zabe ta ƙasa, (INEC) da kuma Gwamnoni. Ya yi bayani dangane da yadda za a gina ƙasa dungurungun don rage zaman kashe wando a tsakanin miliyan goma sha uku na matasa marasa aikin yi kamar yadda hukumar kididdiga ta kasa, (NBS) ta tabbatar.

MANHAJA: Mene ne ra’ayinka dangane da  dimbin matasa marasa aikin yi a ƙasar nan?
ISYAKU IBRAHIM: A matsayina na Uba kuma kaka mai kishin ƙasa, Ina kira da babbar murya ga Shugaban Ƙasaasa Muhammadu Buhari, da hukumar Zaɓe ta INEC da kuma Gwamnonin Jihohi da su yi ɗamara dangane da shawo kan manyan matsalolin da ke addabar ƙasar nan. Banda Nijeriya, babu wata ƙasa a faɗin Duniya da za ta zamo tana da yawan matasa da suka kai miliyoyi suna gararamba. A cikinsu, waɗanda ba su da ilimi ko wata sana’a ƙwaƙƙwara sun fi yawa.

Sannan kuma wasu iyaye sun ɗauki dawainiyar ‘ya’yansu har suka kammala karatun Digiri, amma ba su da aikin yi. Sannan bugu da ƙari, iyayen sun yi murabus daga aiki, har yanzu suna jiran gawon shanu ko kuma uwa kwance, ɗa kwance. Wanda yunwa take sanya matasa shiga ta’addanci gadan-gadan. A ganinina na Dattijo ɗan kishin ƙasa, wannan babban haɗari ne ga zaman lafiyar ƙasa. Yadda Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yake ta fifita zaven baxi ba tare da ya yi ƙoƙarin sama wa matasa aiki ba, ya sa muke ganin yana Yi wa mulkin da zaman lafiyar ƙasa riƙon sakainar kashi.

Ina kira gare shi da ya san cewa, shi Musulmi ne da ya rantse da Alƙur’ani Mai Tsarki, da cewa zai tsare lafiyar ‘yan ƙasa. Lallai Allah ya hore mana albarkatun ƙasa. Idan ka kama hanya daga Abuja zuwa Ƙaramar Hukumar Gwoza da ke jihar Borno, za ka ga filin ƙasa da ba a noma a kai. Maimakon masu mulki su haƙo albarkatun da muke da su, su kuma kambama aikin noma, sun gwammace su yi ta sharholiya da maganar zaɓe. Mu na da gwal, da gagulla da ababe iri daban-daban. Har yanzu ba mu haƙo kashi goma na albarkatun ƙasa ba.

Da Buhari zai dage a haƙo kashi 39 zuwa 40 na ababen da muke da su, da ba ɗan ƙasa da zai je ƙasashen waje neman aiki sai dai jama’ar Duniya su yi rububin zuwa Nijeriya. Ina zargin cewa, Buhari mulki ya sha masa kai ba ya yi wa kasa aiki. Ina yi masa tuni da cewa, kar ya manta ya yi rantsuwa da Alƙur’ani Mai Tsarki. Ina ƙalubalantar Jam’iiyun PDP da APC da su nuna wa jama’a tsarinsu na sama wa dimbin matasa aikin yi. Idan ba haka ba, to su koma su sake shirin kafin zabe. Domin talauci zai sa jama’a da dama ba za su fito zaɓen 2023 ba, kamar yadda aka gani a sauran zaɓuɓɓukan Gwamnoni da na cike gurbi.

Mene ne ra’ayinka dangane da maƙudan kuɗaɗen da aka ware don gudanar da zaɓen baɗi?
(Dariya) Ai hukumar INEC ƙarƙashin jagorancin Farfesa Yakubu ta gudanar da zaɓen da ya shuɗe. Amma Ina zargin ba a ƙididdige ko tantance kuɗin da aka kashe ba. Kuma Majalisar ƙasa ba ta tsawatar ba. Wata kwamacalar sai a Nijeriya! Ko shi tsohon Shugaban INEC, Farfesa Attahiru Jega da ya tsunduma cikin Jam’iyar PRP, idan da Malam Aminu Kano na da rai, da ba zai amince ya shiga Jam’iyar ba.

Wane sharhi za ka yi a kan yadda Gwamnoni suke tafiyar mulki a jihohinsu?
Ina maimakin yadda ba mai binciken yadda Gwamnoni ke facaka da dukiyar jama’a da suke karɓowa daga asusun tarayya. Amma sun yi ruf da ciki a kansu don sun raina jama’a. Lokaci ya yi da Shugaban kwamitin kula da tattalin arzikin ƙasa kuma Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo zai hori Gwamnoni da su biya albashi da yin ayyukan ciyar da ƙasa gaba.

Ana zargin cewa, Wasu tsofaffin gwamnoni da kuma Gwamnoni da ke kan mulki suna ɓoye maƙudan kuɗaɗe ko kuma sun fi jihohinsu kuɗi ba tare da an tambayi inda suka same su ba. Duk mai lura zai fahimci cewa Jama’a ba za su fita su sha Rana ba domin kawai a ce sun jefa ƙuri’u ba ga Gwamnoni da suke ganin kansu kamar Fir’auna ba.

Ina kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa da su warware matsalolin da suka yi wa ƙasar dabaibayi ta hanyar sama wa matasa aiki, sana’o’i, aikin gona, kiwo a cikin yanayi na tsaro don kar a yi wa dimokuraɗiyya mummunar illa ba gaira ba sabab.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *