An yi jana’izar Manjo Janar Rabe mai ritaya a Katsina

Spread the love

Ƙarfe 6.30 na yammacin Asabar aka yi jana’izar Manjo Janaral Rabe Abubakar mai ritaya a unguwar Gidan Dawa da ke cikin Katsina.

Manjo Janaral Rabe Abubakar ya rasu ne a hannun ‘yan bindiga bayan shafe kusan makonni uku shi da Uwargidansa a hannun su.

Bayan rasuwar ne ‘yan bindigan suka sako Uwargidansa tare da gawar mai gidan na ta zuwa bakin hanya a garin Matazu.

Gwamnatin Katsina ta hannun kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro Dr Nasiru Mu’azu Danmusa ya bayana cewa tsohon mai magana da yawun rundunar sojojin Najeriya ya rasu ne sakamakon ciwon Suga da hawan jini da yake fama da su.

Gwamna Dikko Raɗɗa ya nuna alhinin sa kan rasuwar Janaral Rabe wanda ya bayyana a babban rashi ba ma jihar Katsina ba har da ƙasa baki ɗaya.

Ya kuma sha alwashin ganin jami’an tsaro sun yi duk abinda za su iya yi wajen kamo ‘yan bindagan da suka aikata wannan ɗanyan aiki.

Ɗarurruwan jama’a suka halarci Jana’izar marigayin daga baya akai ta tururuwa zuwa gidan sa domin gudanar ta’aziya ga iyalansa.

Mafi yawan mutanen da suka yi ta’aziyar sun bayyana Manjo Janaral Rabe Abubakar a matsayin mutum ne da bai damu da abin duniya ba ga kuma shi da riƙe addini.

By ukarofi

Leave a Reply