
Daga UMAR GARBA a Katsina
An gudanar da sallar jana’izar marigayi Janar Rabe Abubakar (mai ritaya) a birnin Katsina da yammacin ranar Asabar.
An gudanar da sallar jana’izar marigayin ne cikin alhini, inda manyan jami’an gwamnati, shugabannin tsaro, sarakunan gargajiya, ‘yan uwa da abokan arziƙi suka halarta domin yi masa addu’ar samun rahama.
An sace Janar Rabe da matarsa ne a ranar 30 ga watan Mayu a kan hanyar Marabar Musawa zuwa Kafinsoli da ke qaramar hukumar Matazu ta Jihar Katsina.
Mutane da dama sun nuna baqin cikinsu tare da takaici duba da yadda Janar xin ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare qasa amma kuma daga qarshe ya mutu a hannun varayin daji.
Jama’ar Katsina sun kuma nuna damuwa kan tavarvarewar tsaro, inda suka ce rashin tsaro na ci gaba da shafar talakawa da kuma tsoffin jami’an tsaro.
A cikin wata sanarwa, Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta bayyana marigayin a matsayin jajirtaccen soja wanda ya taka muhimmiyar rawa a yaqin da ake yi da ’yan ta’adda.
Rundunar ta ce jajircewarsa za ta ci gaba da zama abin koyi ga dakarun Najeriya.
Saboda haka ne rundunar ta ce za ta ci gaba da qoqari wajen kamo waxanda suka sace marigayin tare da matarsa don su fuskanci hukunci mai tsanani.
A gefe guda, ’yan Najeriya da dama sun yi martani kan lamarin, musamman a shafukan sada zumunta.
Wasu sun nuna damuwa kan tsaron qasa, suna masu tambayar cewa idan har Janar mai ritaya zai iya rasa ransa ta irin wannan hanyar, to waye zai kare talakawa?
Saboda haka ne suka buqaci gwamnati ta qara qaimi wajen yaqar ta’addanci a qasar nan.


