An shiga rana ta uku a zanga-zangar garkuwa da kashe-kashe a Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ɗaruruwan ‘yan Nijeriya ne suka karaɗe titina a Birnin Tarayya Abuja a rana ta uku a jere domin cigaba da nuna adawarsu ga ƙamarin rashin tsaro a sakamakon garkuwa da mutane da kashe-kashen da kuma munanan hare-hare da ke faruwar a sassan ƙasar.

Masu zanga-zangar, wadanda ke neman gwamnati ta dauki matakan gaggawa wajen inganta tsaro, sun toshe wata gada da ke kan hanyar Karu zuwa cikin Abuja wadda ta haɗa Jihar Nasarawa da Abuja.

Ɗauke da alluna masu dauke da sakonni daban-daban tare da rera wakokin nuna rashin amincewa da yadda ake tafiyar da harkokin tsaro, masu zanga-zangar sun bukaci gwamnati ta sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya dora mata na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Da farko sun taru ne a kan gadar da ke yankin kafin daga bisani su yi tattaki zuwa Nyanya domin ci gaba da isar da sakonsu.

Zanga-zangar ta haddasa cunkoson ababen hawa mai tsanani a kan hanyar Abuja–Keffi Expressway, lamarin da ya sa matafiya da dama suka makale na tsawon sa’o’i kafin samun damar wucewa.

Masu zanga-zangar sun ce za su ci gaba da matsa lamba har sai an dauki matakan da za su kawo karshen sace-sacen mutane da kashe-kashen da ke addabar al’umma.

By Babaji