
Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ta bayar da izinin kama tsohon Ministan Ƙirƙira, kimiyya da fasaha, Uche Nnaji, bisa zargin sa da amfani da takardun karatu na bogi.
Rahotanni sun nuna cewa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ta kasa (ICPC) ce ta nemi kotun ta bayar da umarnin kama Nnaji bayan ya gaza amsa gayyatar da hukumar ta yi masa domin gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi masa.
A hukuncin da ta yanke, kotun ta amince da dukkan buƙatun da ICPC ta gabatar, ciki har da ba da damar ayyana Nnaji a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo ta kafafen yaɗa labarai da sauran hanyoyin sadarwa.
Haka kuma kotun ta bawa jami’an ICPC da sauran hukumomin tsaro ikon kama shi a duk inda aka gano shi tare da miƙa shi ga hukumar domin ci gaba da bincike.
Nnaji ya kasance Minista a gwamnatin Tinubu, bayan nadin da aka yi masa a watan Agustan 2023.
Sai dai daga bisani ya sauka daga muƙaminsa bayan zarge-zargen cewa ya gabatar da takardun karatu na bogi a lokacin tantance shi domin zama minista.
Haka kuma, tsohon ministan ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar adawa ta PDP.
