Yobe: Gwamna Buni ya naɗa Yerima Ibn Mahmud sabon sarkin Ngazargamu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da naɗin Alhaji Yerima Ibn Mahmud a matsayin sabon Sarkin Masarautar Ngazargamu da ke jihar.

Sakataren Gwamnatin Yobe na riƙo, Dakta Mohammed Goje ne ya sanar da haka a yau Asabar bayan rasuwar Alhaji Tijjani Ibn Saleh Geidam, wanda ya rasu a Misra bayan tsawon lokaci yana jinya.

A ranar Juma’a ne aka binne marigayin a Damaturu, Babban Birnin Jihar Yobe, kamar yadda Blueprint.ng ta ruwaito.

Gabanin naɗin nasa, sabon Mai Ngazargamun shi ne Turakin Ngazargamu na tsawon shekaru 17 kuma mamba ne a majalisar dokokin jihar.

Haka kuma, ya riƙe manyan muƙamai da dama a majalisar zartarwar jihar da kuma zama kwamishinan ci-gaban harkokin kiwo na Yobe.

Mai Girma Gwamna Mai Mala ya taya sabon sarkin da Masarautar Ngazargamu murna, yana mai kira a gare shi da ya yi amfani da matsayinsa wajen ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya mai ɗorewa da kuma ci-gaban tattali a yankin da ma jihar baki ɗaya.

Ya kuma yi kira ga al’umma da su ba shi goyon baya don cimma nasarori a jagorancin nasa.

By Babaji

Leave a Reply