
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A halin yanzu an shiga rana ta goma a aikin jigilar alhazan Nijeriya na koma wa jihohinsu bayan nasarar kammala aikin hajjin 2026, kamar yadda Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON) ta bayyana.
A yayin haɗa wannan rahoto, jimillar alhazai guda 17,347 ne aka mayar da su Nijeriya daga ƙasa mai tsarki, Saudiyya. A sakamakon haka wasu jihohi sun kammala karɓar nasu alhazan.
A wata sanarwa da hukumar gudanarwar hukumar ta fitar a ranar Asabar, 13 ga Yuni, 2026, NAHCON ta ce jihohin da suka kammala karɓar mahajjatansu sun haɗa da Nasarawa, Gombe, Kogi, Oyo, Osun, Ogun, Jigawa, Kwara da kuma Filato, yayin da Legas, Kebbi da Abuja suka kai matakin kaso 65 zuwa 80 na aikin.
Saidai, sanarwar ta bayyana cewa, wasu jihohin har yanzu ba su fara jigilar dawo da mahajjatansu ba saboda tsarin NAHCON na wanda ya fara zuwa shi zai fara koma wa gida, tana mai bayar da misali da jihohin kudancin Nijeriya da suka tashi daga ƙasar a ranar 19 ga Mayu, 2026 da wasu jihohi da suka bar Nijeriya a ranakun 14 da 16 na watan.
Waɗanda ba a fara jigilar dawowar alhazansu ba sune Adamawa, Bayelsa, Benuwai, Borno, Kuros-Riba, Delta, Edo, Ekiti, Inugu, Imo, Kaduna, Kano, Katsina, Neja, Sakkwato, Taraba, Yobe da kuma Zamfara.
NAHCON ta shawarci kamfanonin jiragen sama da aka ba aikin jigilar da su tabbatar da kammalawa cikin kwanaki 19 kamar yadda aka yi yarjejeniya tsakaninsu da ita.
Tuni dai shugaban hukumar, Ambasada Isma’il Abba Yusuf ya tabbatar wa baki ɗaya mahajjata, iyalansu da ɗaukacin al’umma cewa kowane alhaji zai koma Nijeriya akan lokaci, yana mai fafan za su cimma hakan kafin 30 ga Yuni da Saudiyya ta ware a matsayin ranar ƙarshe na jigilar.
A ƙarshe, NAHCON ta yi wa alhazai, iyalansu kamfanonin jiragen sama da dukkan masu ruwa da tsaki godiya bisa haɗin kai da suka bayar tare alƙawarin cigaba da fitar da bayanan halin da ake cikin akan aikin hajjin na bana.
