Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Katsina ta sanar da rasuwar Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya wanda yayi kusan mako uku a hannun ‘yan bindiga shi da uwargidansa.
Wata sanarwa da ta fito daga ma’aikatar cikin gida da tsaro ɗauke da sa hannun kwamishinan ma’aikatar, Dr Nasiru Mu’azu Ɗanmusa ya sanya wa hannu ya ce Marigayi Manjo Janar Rabe ya rasu yana hannun ‘yan bindiga bayan gajeruwar rashin lafiya.
Dr Nasiru Ɗanmusa ya bayyana cewa marigayin wanda ke ɗauke da cutar suga da hawan jini ya sami wata yar matsala da cutar.
Kafin dai rasuwar sa, kwamishinan ya ce jami’an tsaro sun yi duk abinda za su iya yi domin ceto sa da mai ɗakin sa amma Allah bai nufa ba.
Kwanan baya ne ‘yan bindiga suka kama marigayin tare da matar sa har da direban su a hanyar garin Matazu bayan hare haren bindiga da suka kai wa motar sa.
Gwamnan Katsina Malam Dikko Raɗɗa ya bayana rasuwar Janar Rabe a matsayin babban rashi bama ga al’ummar jihar Katsina ba har ma da ƙasa baki ɗaya.
Ya Kuma jaddada ƙudirin gwamnatin sa da haɗin gwiwar gwamnatin tarayya na yin duk abinda za su iya yi na ganin sun kawo ƙarshen wannan ta’addanci bama a Katsina ba har da wasu sassan ƙasar.
Babu dai wani bayani game da halin da uwargidan sa wadda yanzu haka tana hannun yan bindigan,sai da shi direban motar su wanda yake ɗauke da raunin sakamakon harbin ‘yan bindaga, ya kuɓuta.
.
