Manjo Janar Rabe ya rasu a hannun ‘yan bindiga

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Tsohon kakakin rundunar sojin Nijeriya, Manjo Janar Rabe Abubakar (mai ritaya) ya rasa ransa a hannun ‘yan bindiga.

Kwamishinan tsaron jihar Katsina Dr. Nasuru Ma’azu Damnusa ne ya tabbatar da mutuwar ta sa, inda yanzu haka ana shirye shiryen xauko gawarsa daga dajin da ake tsare da shi.

‘Yan bindiga masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa, sun sace tsohon Janar xin tare da matarsa a hanyar Matazu a yayin da suke cikin mota don halarta xaurin aure.

Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana cewa ya rasu ne yayin da yake hannun ‘yan bindiga duk da qoqarin da gwamnati da hukumomin tsaro suka yi domin ganin an kubutar da shi lafiya.

A cikin sanarwar da Kwamishinan tsaro Dr. Nasiru Mu’azu, ya fitar, gwamnatin ta ce marigayin ya rasu ne sakamakon matsalolin rashin lafiya da suka haxa da ciwon sukari da hawan jini.

Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana alhinin sa kan lamarin, yana mai cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da haxin gwiwa da gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro domin kawo qarshen matsalar ‘yan bindiga tare da tabbatar da an hukunta masu hannu a wannan mummunan lamari.

By Babaji

Leave a Reply