Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
’Yan Nijeriya da dama sun yi wa Babban Daraktan Kamfanin Sadarwa na MTN, Karl Toriola, martani mai zafi bayan ya bayyana cewa tsarin intanet marar iyaka, wato unlimited data, kusan babu shi a duniya sai idan mai amfani yana biyan kuɗi masu yawa.
Toriola ya yi wannan bayani ne a wani taron manema labarai mai taken “Data on Trial” da aka gudanar a Legas ranar Asabar, inda ya mayar da martani kan matsin lambar da masu amfani da layukan sadarwa ke yi na neman intanet mai rahusa da kuma tsarin unlimited data.
A cewarsa, abin da mutane ke kira unlimited data a kasuwannin duniya ba ya wanzuwa a mafi yawan lokuta, sai dai ga masu biyan kuɗaɗe masu tsada da yawancin jama’a ba za su iya ɗauka ba.
Ya bayyana cewa tsarin sadarwar wayar hannu ba zai iya ɗaukar buƙatar unlimited data mai rahusa ba, domin hakan zai jawo matsala ga ingancin sabis da kuma ci gaban kayayyakin more rayuwa da ake buƙata wajen gudanar da aikin.
“Batun unlimited data a layukan wayar hannu ba ya wanzuwa a ko ina cikin duniya sai idan mutum yana biyan kusan dala 400 a wata ko makamancin haka. Akwai manyan nau’ikan data ne kawai tare da ƙa’idojin amfani,” inji shi.
Ya ƙara da cewa, ba zai yiwu a samar da isasshen ƙarfin cibiyar sadarwa da zai bai wa kowa unlimited data ba tare da lalata ingancin sabis ba.
Domin ƙarfafa hujjarsa, Toriola ya kwatanta lamarin da harkar sufurin jiragen sama, yana mai cewa idan aka bai wa kowa damar yin tafiye-tafiye marasa iyaka a farashi mai rahusa, masana’antar jiragen sama ba za ta iya ɗorewa ba.
Martanin ’yan Nijeriya:
Sai dai kalaman nasa sun fusata mutane da dama a kafafen sada zumunta, inda wasu suka zargi MTN da cin zarafin masu amfani da sabis ɗinsa tsawon shekaru.
Wani mai amfani da kafar ɗ mai suna Archangel Michael (@willofgodd) ya rubuta cewa: “MTN ya daɗe tana amfani da ’yan Nijeriya. Majalisar Dokoki ta yi shiru saboda ana ba su data da kati kyauta da kuma hannun jari a kamfanin.”
Shi kuwa @_Judlaw ya yi watsi da kalaman shugaban MTN, yana mai cewa ƙasashe da dama suna da tsarin unlimited data mai sauƙin farashi.
A cewarsa, ƙasar Finland tana da tsarin unlimited data da ya bazu sosai, yayin da a Birtaniya ake samun unlimited 5G a kan fam 15 zuwa 20 kacal a wata, sannan Faransa na da irin wannan tsari a tsakanin euro 20 zuwa 30.
Ya ce, matsalar ba wai rashin wanzuwar unlimited data ba ce, illa dai batun farashi da gasa a kasuwa.
Wani mai amfani da suna @Mrboorish ya ce shugaban MTN yana anfani da rashin sanin yadda kasuwannin ƙasashen waje ke aiki.
“Yawancin ’yan Nijeriya ba su taɓa fita ƙasashen waje ba, shi ya sa ake iya yaɗa irin waɗannan bayanai ba tare da an ƙalubalanta su ba,” inji shi.
Haka kuma, wasu sun kwatanta MTN da kamfanin Airtel, suna masu cewa Airtel na bayar da abin da ya fi kama da unlimited data.
Wani mai suna @OmonWallz ya rubuta cewa, “Airtel za ta ga wannan magana ta yi dariya, domin tasu unlimited data gaskiya ce.”
Shi kuma @olamy96 ya tambayi dalilin da ya sa MTN ke amfani da kalmar “unlimited” idan akwai iyaka a amfani da sabis ɗin.
Sowore ya yi barazanar zanga-zanga:
A wani ci gaba kuma, ɗan gwagwarmaya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC a zaɓen 2027, Omoyele Sowore, ya yi barazanar shirya zanga-zangar ƙasa baki ɗaya kan kalaman shugaban MTN.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na ɗ, Sowore ya bayyana kalaman Toriola a matsayin ƙarya, yana mai cewa miliyoyin mutane a duniya suna anfani da unlimited data ko makamancin haka a farashi mai sauƙi idan aka kwatanta da abin da ’yan Nijeriya ke biya.
Ya ce, “Mutane miliyoyi a duniya suna anfani da unlimited data a farashi mai rahusa idan aka kwatanta da kuɗin shiga na jama’a, fiye da yadda ake yi a Nijeriya.”
Sowore ya kuma soki tsadar kuɗin sadarwa da matsalolin ingancin sabis a Nijeriya, yana mai cewa ’yan ƙasa sun cancanci samun sadarwa mai araha da inganci.
Ya ƙare da cewa, “Lokacin da za a yi #OCCUPYMTN a faɗin ƙasar nan yana ƙaratowa.”
