Gwamnatin Tarayya ta saki biliyan 700 don biyan ’yan kwangila 1,240

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya ta amince da biyan kuɗaɗe ga ’yan kwangila sama da 1,240 a wani mataki da ake sa ran zai farfaɗo da harkokin kasuwanci tare da ƙarfafa tattalin arziki a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Rahotanni sun bayyana cewa Ministan Kuɗi kuma Mai Kula da Harkokin Tattalin Arziki na ƙasa, Wale Edun, ne ya amince da biyan kuɗaɗen bayan kammala wani tsauraran bincike da tantance bayanai domin tabbatar da cewa dukkan buƙatun da aka amince da su sahihai ne kuma sun cika sharuɗɗan biyan kuɗi.

A cewar ma’aikatar, kuɗaɗen sun shafi ’yan kwangilar da ke aiki da Ma’aikatu, Hukumomi da Sassan Gwamnatin Tarayya, kuma hakan wani muhimmin mataki ne na rage tarin basussukan da gwamnati ke bin ’yan kwangila, musamman kamfanonin cikin gida da ƙananan da matsakaitan masana’antu.

Ma’aikatar ta bayyana cewa a wannan karon an bai wa fifiko ga ’yan kwangilar da ke da sahihin bashin da bai wuce Naira miliyan 100 ba. Hakan na nuna ƙoƙarin gwamnati na tabbatar da cewa tallafin ya isa ga manyan sassa na harkokin kasuwanci maimakon ya ta’allaka ga wasu tsirarun manyan kamfanoni kaɗai.

Jami’an gwamnati sun ce fitar da kuɗaɗen zai taimaka wa ɗaruruwan kamfanoni su koma wuraren ayyukansu, su biya ma’aikatansu albashi, su daidaita basussukan da suke bin masu samar musu da kayayyaki da kuma cika sauran nauye-nauyen kuɗi da ke kansu.

A cewar ma’aikatar, wannan mataki ya nuna aniyar Gwamnatin Tarayya ta mayar da manufofin tattalin arziki zuwa ainihin sakamako ta hanyar biyan basussukan da aka gada cikin gaskiya da bin ƙa’idojin kashe kuɗin gwamnati.

Ma’aikatar ta kuma bayyana cewa a cikin watannin baya-bayan nan gwamnatin ta biya sama da Naira biliyan 700 na basussukan da aka tabbatar da sahihancinsu ga ’yan kwangilar cikin gida.

Har ila yau, ta ce a watan Mayun 2026 kaɗai an sarrafa biyan kuɗaɗe da suka kai kusan Naira biliyan 436.6, abin da ta bayyana a matsayin babban ci gaba wajen sakin kuɗaɗe cikin tattalin arziki domin ƙarfafa kasuwanci da bunƙasa ci gaban ƙasa.

Gwamnatin ta yi nuni da cewa mayar da hankali ga yawan ƙananan ’yan kwangila zai tabbatar da cewa tasirin kuɗaɗen ya bazu zuwa fannoni da yankuna daban-daban na ƙasar nan.

Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya ta ce wannan biyan kuɗaɗe zai ƙara wa ’yan kwangila, masu samar da kayayyaki da masu ba da ayyuka ga gwamnati kwarin gwiwa, tare da nuna cewa gwamnati na da niyyar cika dukkan wajibanta na kuɗi da aka tantance.

A cewarta, ga yawancin waɗanda za su amfana, kuɗaɗen ba kawai biyan bashi ba ne, domin za su taimaka wajen ci gaba da gudanar da kasuwanci, kare ayyukan yi, kammala ayyukan da ake yi da kuma bayar da gudunmawa ga farfaɗowar tattalin arzikin ƙasa.

Ma’aikatar ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da kiyaye tsauraran matakan kula da kuɗaɗen gwamnati tare da tabbatar da cewa ana biyan dukkan basussukan da aka tabbatar da sahihancinsu cikin lokaci da gaskiya.

By ukarofi

Leave a Reply