Dalibar jami’a ta rasu bayan kammala jarrabawar ƙarshe a Kogi

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wata ɗaliba a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kogi (Kogi State Polytechnic), mai suna Mariam Saliu, ta rasu bayan ta faɗi ba zato ba tsammani sa’o’i kaɗan bayan gama bikin murnar kammala jarrabawar ƙarshe ta karatunta.

Rahotanni sun bayyana cewa Mariam ta rasu ne a ranar 9 ga Yunin 2026, bayan da tun da farko ta bayyana farin cikinta a shafukan sada zumunta sakamakon kammala jarrabawar da ta yi na ƙarshe.

A wani saƙo da ta wallafa a Facebook da misalin tsakar rana, marigayiyar ta nuna murnar kai ƙarshen tafiyar karatunta inda ta rubuta: “Alhamdulillah. Hawaye na farin ciki. A ƙarshe dai na gama.”

Sai dai abin da ya fara a matsayin murna ya rikiɗe zuwa babban rashi mai tayar da hankali.

Bisa rahotanni, Mariam ta faɗi ne yayin da take murnar kammala karatu tare da abokan karatunta jim kaɗan bayan ta gama rubuta takardar jarrabawar warshe. Daga bisani aka tabbatar da rasuwarta.

Wani mai amfani da Facebook mai suna Ohida Bill-Ikis ya ce marigayiyar ta faɗi ne a tsakiyar abokan karatunta yayin bikin “sign-out” da ɗalibai ke yi bayan kammala karatu.

“Ta fazi ne a tsakiyar abokan karatunta da ke gudanar da bikin kammala karatu. Wannan ne abin da ya faru,” inji shi.

Kafin rasuwarta, Mariam ta kasance shugabar ɗaliban Ebira ta ƙungiyar ɗalibai Ebira ta Nijeriya (NAES), reshen Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kogi, inda kwanaki kaɗan kafin mutuwarta ta wallafa saƙon godiya bayan kammala wa’adinta na jagoranci.

A cikin saƙon, ta gode wa iyalai, abokai da duk masu goyon bayanta da suka tsaya mata a lokacin da take jagorantar ƙungiyar.

Bayan labarin rasuwarta ya bazu, shafin da ta yi amfani da shi wajen bayyana murnar kammala karatu ya koma wurin jimami, inda saƙonnin taya murna suka rikiɗe zuwa addu’o’i da alhini.

Daudu Marygold, ɗaya daga cikin masu jimami, ta bayyana rasuwar a matsayin babban abin takaici.

“Wannan ya yi min ciwo. Wannan azaba ce mai raɗaɗi. Mariam, Mariam! Na ga saƙon da kika wallafa game da nasarar karatunki kuma ina shirin taya ki murna. Ban san cewa zai zama saƙon ta’aziyya ba. Iyalanmu sun yi rashin wata baiwar Allah,” inji ta.

Shi ma Ezekiel Oyiza ya bayyana mamakinsa da yadda lamarin ya sauya cikin kankanin lokaci.

“Ya Allah! Wane irin labari ne wannan? Ban ma san ko zan rubuta taya murna ne ko kuma addu’ar neman rahama ba.”

Muhammad Jibrin Etsu kuwa ya ce lamarin ya sake tunatar da jama’a cewa rayuwar duniya ba ta da tabbas.

“Haƙiƙa babu abin da ya fi wucewa kamar rayuwar duniya, kuma babu abin da ya fi tabbata kamar mutuwa.”

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a bayyana a hukumance musabbabin rasuwar Mariam Saliu ba.

By ukarofi

Leave a Reply