Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ta ɗaukaka ƙara a Kotun ɗaukaka ƙara domin ƙalubalantar wasu hukunce-hukuncen Babbar Kotun Tarayya guda biyu da suka yi saɓani kan ikon hukumar na tsara jadawalin gudanar da zaɓukan shekarar 2027.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN), ya bayyana hakan ne a taron tuntuba na biyu na wannan shekara da hukumar ta gudanar da shugabannin jam’iyyun siyasa a hedikwatarta da ke Abuja.
Amupitan ya ce matakin ɗaukaka ƙarar ya zama dole domin tabbatar da daidaito, tabbas da kuma ingantaccen shiri gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Ya bayyana cewa ɗaya daga cikin hukunce-hukuncen ya fito ne daga shari’ar Youth Party da INEC mai lamba FHC/ABJ/CS/517/2026, wadda ta yi tambaya kan wasu lokutan da INEC ta tsara a jadawalin zaɓen 2027.
A ɗaya ɓangaren kuma, ya ce a shari’ar SDP da INEC mai lamba FHC/ABJ/CS/720/2026, kotun ta tabbatar da ikon INEC na tsara harkokin zaɓe, amma ta soke wasu lokutan da suka shafi gabatar da sunayen ’yan takara da maye gurbinsu.
A cewarsa, duk da cewa hukumar na mutunta hukunce-hukuncen kotuna, akwai muhimman tambayoyin doka da suka taso dangane da iyakar ikon da kundin tsarin mulki da dokokin zaɓe suka bai wa INEC wajen tsara da gudanar da ayyukan zaɓe.
“Saboda saɓanin da ke tsakanin waɗannan hukunce-hukuncen, kuma domin tabbatar da tabbas da kwanciyar hankali a shirye-shiryen zaɓen 2027, hukumar ta shigar da ƙorafe-ƙorafe a Kotun ɗaukaka ƙara,” inji shi.
Shugaban INEC ya bayyana cewa ayyukan zaɓe suna da alaƙa da juna, kuma ba za a iya gudanar da su a matsayin abubuwa masu zaman kansu ba.
Ya ce duk da cewa Dokar Zaɓe ta tanadi wa’adin wasu ayyuka, akwai wasu muhimman ayyuka da ba a fayyace wa’adinsu a doka ba, amma dole ne a tsara su cikin daidaito domin kauce wa rudani.
Daga cikin irin waɗannan ayyuka akwai tantance rajistar jam’iyyun siyasa, sa ido kan zaɓukan fidda gwani, shirya na’urorin BVAS da kuma buga muhimman kayayyakin zaɓe.
Amupitan ya tabbatar wa jama’a da jam’iyyun siyasa cewa duk da ƙarar da ake yi a kotu, INEC za ta gudanar da zaɓen 2027 cikin cikakken bin kundin tsarin mulki, Dokar Zaɓe da kuma duk wani sahihin hukuncin kotu.
Ya kuma sanar da cewa daga ranar 26 ga Yuni, 2026, hukumar za ta bai wa dukkan jam’iyyun siyasa lambobin shiga tsarin yanar gizo na gabatar da sunayen ’yan takara.
A cewarsa, lambobin za su bai wa jami’an jam’iyyu damar shigar da sunaye, bayanan sirri da sauran bayanan da ake buƙata game da ’yan takararsu.
Ya buƙaci jam’iyyun siyasa da su tabbatar da cewa jami’ansu na fasahar sadarwa da sauran masu ruwa da tsaki sun shirya yadda ya kamata domin kammala dukkan bayanan kafin wa’adin da aka ƙayyade.
Haka kuma, shugaban INEC ya yi kira ga jam’iyyun siyasa da su ƙara wayar da kan jama’a da kuma ƙarfafa masu cancantar yin rajistar zaɓe domin su yi anfani da shirin ci gaba da rajistar masu kaɗa ƙuri’a tare da karɓar katin zaɓensu na dindindin (PVC).
Sai dai ya nuna damuwa kan yawaitar rikice-rikicen shugabanci a cikin jam’iyyun siyasa da ke gaban kotuna, yana mai cewa hakan na kawo cikas ga tsarin dimokuraɗiyya.
A ƙarshe, Amupitan ya buƙaci jam’iyyun siyasa da su mutunta doka, su gudanar da zaɓukan fidda gwani cikin gaskiya da adalci, su guji tayar da hankali, kalaman ƙiyayya da sayen ƙuri’u, tare da mayar da hankali kan kamfen da suka shafi manufofi da ci gaban ƙasa.
