Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Janar Manajan Kamfanin Audu Manaja, Alhaji Sulaiman Hussain, ya bayyana rasuwar fitaccen ɗan kasuwa kuma hamshaƙin mai harkar man fetur, Alhaji Abdullahi Ahmad (Audu Manaja), a matsayin babban rashi ga al’ummar Arewa da Nijeriya baki ɗaya.
Da yake zantawa da manema labarai, Alhaji Sulaiman Hussain ya ce marigayin mutum ne mai nagarta, gaskiya da riƙon amana, wanda ya yi fice wajen kyakkyawar mu’amala da jama’a a harkokin kasuwanci da zamantakewa.
Ya ce marigayin ya kasance mutum mai cika alƙawari da yafiya, yana kuma kula da ma’aikatansa kamar ’ya’yansa na jini.
“Duk wanda ya san Audu Manaja zai shaida cewa mutum ne mai gaskiya da riƙon amana. Ba ya karya alƙawari, kuma idan wani abu zai hana cika alƙawarin da ya yi, tun kafin lokaci zai sanar da kai. Mu da muke aiki tare da shi ya riƙe mu kamar ’ya’yansa,” inji Sulaiman Hussain.
Ya bayyana cewa marigayin ya rasu ya bar mata uku da ’ya’ya sama da 30, ciki har da maza 17 da mata 19, inda ya ce ɗaya daga cikin ’ya’yansa mata ta rigaya ta rasu.
A cewarsa, duk da cewa Audu Manaja ya daɗe yana fama da rashin lafiya, ya yi wasu shawarwari da wasiyyoyi kafin tafiyarsa zuwa neman lafiya, lamarin da ya nuna kamar ya fahimci cewa ajalinsa ya kusa.
“Mun yi matuƙar alhini da wannan rashi. Allah Ya jiƙansa da rahama, Ya gafarta masa kurakuransa,” ya ƙara da cewa.
Sulaiman Hussain ya bayyana marigayin a matsayin ɗaya daga cikin manyan ’yan kasuwar man fetur a Nijeriya, wanda ya gina babbar daular kasuwanci da ta samar wa dubban mutane ayyukan yi.
Ya ce Audu Manaja ya mallaki gidajen mai da dama a faɗin ƙasar nan tare da manyan ofisoshi a jihohi daban-daban, baya ga motocin ɗaukar mai sama da 150 da ke aiki a ƙarƙashin kamfaninsa.
“A kowace mota akwai direba da mataimaka biyu. Wannan ya nuna irin gudunmawar da yake bayarwa wajen samar da ayyukan yi. Rasuwarsa ta bar babban giɓi a harkar mai wanda ba zai yi sauƙin cikewa cikin gaggawa ba,” inji shi.
Ya kuma ce rasuwar marigayin ta girgiza Kano, Arewa da Nijeriya baki ɗaya, musamman idan aka yi la’akari da yawan jama’ar da suka halarci jana’izarsa da kuma waɗanda suka kai ziyarar ta’aziyya daga sassa daban-daban na ƙasar nan.
A ƙarshe, ya gode wa dukkan waɗanda suka halarci jana’izar da kuma waɗanda suka jajanta wa iyalan marigayin, yana addu’ar Allah Ya gafarta wa Audu Manaja, Ya sa Aljannar Firdausi ta zama makomarsa, tare da bai wa iyalansa da al’ummar Kano haƙurin jure wannan babban rashi.
