Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Sarkin Ibo na Hausawan Afirka, Ambasada (Dakta) David N. Onwere, ya yi kira ga al’ummar Jihar Kano da Nijeriya bakiɗaya da su guji gina gine-gine akan magudanan ruwa, yana mai cewa, yin hakan na haddasa matsalolin muhalli da kuma ambaliyar ruwa.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai bayan karɓar gaisuwar Babbar Sallah daga al’ummar Musulmi a fadarsa da ke unguwar Nomansland a Kano.
Sarkin ya kuma buƙaci jama’a su rika tsaftace magudanan ruwa tare da guje wa zubar da shara a cikinsu domin rage hadarin ambaliya da kare muhalli.
Ya yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, bisa kokarin da gwamnatinsa ke yi wajen tsaftar muhalli a duk karshen wata, da kuma ayyukan ci gaban da suka hada da gyaran hanyoyi da samar da fitulun kan tituna a sassan jihar.
Daga ƙarshe, ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da bai wa gwamnatin Abba Kabir Yusuf hadin kai da goyon baya, tare da godiya ga Allah Madaukakin Sarki bisa zaman lafiyar da ake samu a jihar Kano.
