Ranar Dimukraɗiyya: Gwamnan Kaduna ya saki fursunoni 97, ya tallafa musu da jari

Spread the love

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya saki fursunoni 97 da ke Gidan gyaran hali na Kaduna, inda ya ba su ‘yanci tare da tanadar musu tallafin kuɗi da damar koyon sana’o’i domin fara sabuwar rayuwa.

Da yake jawabi a wajen bikin da aka gudanar a gidan gyaran halin Kaduna, Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa ranar 12 ga Yuni wata rana ce mai muhimmanci a tarihin Nijeriya, wadda ke tunatar da al’umma irin sadaukarwar da jaruman dimokuraɗiyya suka yi wajen tabbatar da mulkin farar hula da ‘yancin jama’a.

Gwamnan ya ce sakin fursunonin ya biyo bayan amfani da ikon afuwa da kundin tsarin mulkin ƙasa ya ba shi, bayan shawarwarin Kwamitin ba da Afuwa na Jihar Kaduna wanda ya tantance waɗanda suka cancanci cin gajiyar shirin.

A cewarsa, shirin ya haɗa da sakin wasu gaba ɗaya, rage wa wasu hukunci da kuma biyan tara ga wasu domin su samu damar komawa cikin al’umma.

Uba Sani, wanda ya kasance cikin masu fafutukar neman dimokuraɗiyya a baya, ya yi jinjina ga marigayi Cif MKO Abiola, Cif Gani Fawehinmi, Dakta Beko Ransome-Kuti, Hajiya Kudirat Abiola da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, tare da sauran jaruman da suka sadaukar da rayuwarsu wajen tabbatar da dimokuraɗiyya a Nijeriya.

Ya ce sadaukarwar da suka yi ta nuna cewa ‘yanci da dimokuraɗiyya abubuwa ne da ya kamata a ci gaba da karewa da bunƙasa su domin amfanin al’umma.

Domin tabbatar da cewa waɗanda aka saki sun samu kyakkyawar makoma, gwamnan ya sanar da bayar da tallafin kuɗi ga dukkan fursunonin 97 da aka yi wa afuwa, tare da ba su damar shiga cibiyoyin koyon sana’o’i na gwamnatin jihar da ke Soba, Rigachikun da Samaru-Kataf domin koyon sana’o’in da za su dogara da kansu.

Ya jaddada cewa gwamnatin sa ta yi imani da gyaran hali, ba wai hukunci kaɗai ba, yana mai cewa kowa na da damar sauya rayuwarsa idan aka ba shi dama.

Gwamnan ya kuma yi kira ga sarakuna, malamai, shugabannin al’umma da sauran jama’a da su karɓi waɗanda aka saki hannu bibbiyu tare da taimaka musu wajen sake shiga rayuwar yau da kullum.

A wani mataki na tallafawa gyaran hali, Gwamna Uba Sani ya amince da bayar da motar aiki ga Hukumar Kula da gidajen gyaran hali ta Nijeriya reshen jihar Kaduna, tare da ba da kayan aikin lafiya da magunguna domin inganta kula da lafiyar fursunoni.

Tun da farko, Babban Lauyan Jihar Kaduna kuma Kwamishinan Shari’a, Barista James Kanyip, ya bayyana matakin a matsayin wata alama ta shugabanci mai tausayi da hangen nesa na Gwamna Uba Sani.

Ya ce ikon afuwa wata muhimmiyar hanya ce ta haɗa adalci da jin ƙai, tare da taimakawa wajen rage cunkoso a gidajen gyaran hali da kuma bai wa mutane damar sake gina rayuwarsu.

By Babaji

Leave a Reply