Kwamitin zartarwar ƙungiyar shirya finafinan Arewa ya gudanar da taron ƙasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kwamitin Zartaswa na Ƙasa (NEC) na Ƙungiyar Masu Shirya Finafinan Arewa ya gudanar da babban taro da ya haɗa mambobinsa daga sassa daban-daban.

An gudanar da taron ne a ranar Talata, 9 ga watan Yuni, 2026, wanda aka yi da nufin sauya fasalin ƙungiya da kuma samar da hanyoyin ƙarfafa harkokin bisa tsari mai kyau.

Shugaban ƙungiyar, Salisu Mohammed Officer, a wata takarda da Sakataren ƙungiyar Sani Sule Katsina ya fitar, ya jaddada muhimmancin haɗin kai akan lamuran buƙatun masana’antar shirya finafinai da kuma ɗaukacin al’umma, wanda ka iya haifar da gagarumar ci-gaba ga lamuran ƙungiyar.

Sule Katsina ya ce taron ya ƙunshi tattaunawa akan nazarin tsarin shugabancin AFMAN a matakin ƙasa da jihohi, sake fasali da tsarin ƙungiyar, ƙarfafa tsarin gudanarwa da hulɗa da mambobi da kuma tattauna batutuwan da suka taso da hanyoyin ci-gaba.

Kazalika, kwamitin ya amince da gudanar da taron Kwamitin Zartaswa na Ƙasa a ƙarshen kowane wata, ko dai ta hanyar taro na zahiri ko na yanar gizo, domin tabbatar da ci gaba da tattaunawa da kuma aiwatar da shawarwarin da aka yanke.

Bugu da ƙari, kwamitin ya yi kira ga dukkan mambobin AFMAN a faɗin Arewacin Nijeriya da su rungumi sulhu, haɗin kai da fahimtar juna domin ci
gaban ƙungiyar baki ɗaya, yana mai ƙarfafa musu gwiwa da su haɗa hannu wajen ƙarfafa AFMAN da kuma mayar da ita ƙungiya mai anfani ga mambobinta, musamman a daidai lokacin da ƙasar ke tunkarar muhimmin zangon siyasa.

A ƙarshe, shugaban ya yi godiya ga dukkan mahalarta bisa jajircewa da gudummawar
da suka bayar domin cigaba da bunƙasa AFMAN.

By Babaji

Leave a Reply