Sojoji sun halaka jagoran ISWAP, Khalifa yayin da kwamandoji biyu suka miƙa wuya a Borno

Spread the love

Wasu manyan da ake zargi mambobin ƙungiyar ta’addanci ta ISWAP guda biyu ciki har da wani ƙwararren mai ƙera boma-bomai da kuma wani kwamanda, sun miƙa wuya ga dakarun sojin Nijeriya a jihar Yobe.

Rahotanni sun bayyana cewa mutanen biyu, da aka bayyana sunayensu da Abu Umar da Ismail Mohammed, sun mika kansu ga sojojin Bataliya ta 159 a garin Geidam ranar 8 ga watan Yuni kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.

Majiyoyin tsaro sun ce Abu Umar na daga cikin fitattun kwararrun ISWAP wajen kerawa da amfani da bama-baman da ake dasawa a cikin motoci domin kai hare-hare.

Sun ce irin wadannan kwararru na taka muhimmiyar rawa a kungiyoyin ta’addanci saboda fasaharsu wajen shirya manyan hare-hare kan sojoji, fararen hula da muhimman cibiyoyin gwamnati.

Haka kuma, an bayyana Ismail Mohammed a matsayin wani kwamanda da ke gudanar da ayyukansa a yankin Baa Shuwa da ke cikin dajin Timbuktu Triangle, daya daga cikin manyan maboyar ‘yan ta’adda a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Masu sharhi kan harkokin tsaro sun bayyana mika wuyan a matsayin babban nasara ga rundunar sojin Najeriya a yakin da take yi da kungiyoyin Boko Haram da ISWAP a yankin Tafkin Chadi.

Rahoton ya ce bayanan da wadanda suka mika wuya za su bayar na iya taimaka wa hukumomin tsaro wajen gano wuraren kera bama-bamai, ma’ajiyar makamai, sansanonin horaswa da hanyoyin safarar kayan aiki da ‘yan ta’addan ke amfani da su.

By Babaji

Leave a Reply