Jami’an tsaro sun halaka sanannun jagororin ‘yan bindiga biyu a Jihar Kogi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Alhamis Rundunar ‘Yan sanda a Jihar Kogi, ta sanar da wata gagarumar nasara na mutuwar wani sanannen jagoran ‘yan bindiga mai suna Ibrahim Baccujo bayan wani ba-takashi da jami’an tsaro a jihar.

Al’amarin ya auku ne a lokacin jami’an suka yi yunƙurin daƙile garkuwa da wasu tarin ɗalibai da ke rubuta jarrabawar WAEC a makarantar sakandare ta Iluke da ke Ƙaramar Hukumar Kabba-Bunu a ranar 10 ga Yuni, 2026.

A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’ar rundunar, ASP Saliu Oyiza Afusat ya fitar, ya ce Baccujo na ɗaya daga cikin ‘yan bindigar da suka yi rashin nasara wajen garkuwa da ɗaliban da kuma wasu mutane a yankin.

Ya bayyana cewa, bayyanan sirri sun nuna cewa a ranar da al’amarin ya faru jagoran ‘yan bindigar ya jikkata daga raunukan harbin bindiga da ya samu a yayin musayar wuta da jami’an tsaro a sa’ilin da suka amsa kiran gaggawa.

Haka kuma, bayanai sun bayyana cewa wani babban ɗan bindiga mai suna Isa Mai Ɗanbaba ya rasa ransa a yayin wani atisaye, lamarin da ya haifar da gagarumar faɗuwa ga masu aikata miyagun laifuka a yankin.

A cewar rundunar, an cimma wannan nasara ne bisa haɗin-gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da suka haɗa ‘yan sanda, sojoji, DSS, Cibil Defence da kuma ‘yan bijilante.

By Babaji

Leave a Reply