
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karrama wasu manyan mutane su 50 da kyautar ƙasa sakamakon rawar gani da suka taka wajen gwagwarmayar kafa dimukraɗiyya a Nijeriya.
Daga cikin waɗanda aka karrama a Ranar Dimukraɗiyyar akwai ‘yan jarida, jagororin fafutukar ‘yancin al’umma da wasu manyan sojoji da suka yaƙi mulkin soji a ƙasar.
Shugaba Tinubu ya sanar da haka ne a saƙonsa na ranar 12 ga Yuni a matsayin ɓangaren harkokin Ranar Dimukraɗiyya.
A cewarsa, ‘yan Nijeriya sun amfana da sadaukarwar ‘yan fafutukar kafa mulkin dimukraɗiyya wajen ba shi kariya da ƙarfafa cibiyoyin harkokinsa.
Ya ce, zaɓen “June 12”, 1993 ya nuna haƙiƙanin haɗin kan da ke tsakanin ‘yan Nijeriya.
Ya bayyana cewa, yayin da magabatan June 12 suka samar da ‘yancin siyasa, wajibi ne akan al’ummar yanzu su yi aiki tuƙuru wajen samar da ‘yancin tattalin arziƙi.
Shugaban ƙasar ya ƙara da cewa, waɗanda aka karrama sun jure wa wahalhalu da sadaukarwar kai yayin gwagwarmayar dawo da mulkin dimukraɗiyya.
Ga jaddawalin waɗanda aka karraman:
Barrister Ayoka Lawani
Tunde Fagbenle
Oladele Alake
Olatunji Bello
Louis Odion
Segun Babatope
Sam Omatseye
Sir Ademola Osinubi
Bola Bolawole
Lade Bonuola
Femi Kusa
Debo Adeniran
Chief Ayo Opadokun
Chief Ralph Obiora
Ose Osayande
Barrister Osa Director
Prof. Sylvester Odion-Akhaine
Dr Arthur Nwankwo (Posthumous)
Dr Osagie Obayuwana
Dr Joe Okei-Odumakin
Barrister Titus Mann
Joe Igbokwe
Richard Akinnola
Ben Charles-Obi (Posthumous)
George Mbah
Dr Niran Malaolu
Major-General Ishola Williams (mai ritaya)
Femi Aborisade
Jenkins Alumona
Gbemiga Ogunleye
Muyiwa Adekeye
Babajide Kolade-Otitoju
Ike Okonta
SOJOJI ‘YAN DIMUKRAƊIYYA
Major General MA Garba
Brigadier General Lawal Jaafaru Isa
Col Umar Farouk Ahmed
Col Sambo Dasuki
Col Lawan Gwadabe
Brigadier Jonathan Ndam Temlong
Col Musa Shehu
Major General Chris Eze
Major General Harris Dzarma
Col Isa Jibrin
Maj. General Joseph Oshanupin
Col Olusegun Oloruntoba, Olugbede na Masarautar Gbede
Lieutenant Colonel Happy Kefas Bulus
Col J Okai
Col Emmanuel Ndubueze
Lt Col Yakubu Muazu
Brigadier Yahaya Abubakar, wanda shi ne Etsu na Nupawa da ke riƙe da kamben CFR.
Shugaban ƙasar a ƙarshe, ya ce za a fitar da cikakken jaddawalin sunayen nan da wasu ‘yan kwanaki.
