Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ce gagarumin ci gaban da aka samu a jihar cikin shekaru da suka gabata shaida ce ta ribar dimokuraɗiyya da kuma amfanin shugabanci mai ɗaukar al’umma a matsayin ginshiƙi tare da riƙon amana.
A saƙonsa na taya murnar ranar dimokuraɗiyya da ya fitar a ranar Juma’a, gwamnan wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin jihohin Arewa (NSGF), ya taya shugaba Bola Ahmed Tinubu da ɗaukacin ‘yan Najeriya murnar cika shekaru 27 ana gudanar da mulkin dimokuraɗiyya ba tare da tangarɗa ba.
Ya bayyana dimokuraɗiyya a matsayin hanya mafi inganci da Najeriya za ta iya bi wajen samun ci gaba mai ɗorewa, yana mai cewa nasarorin da ake gani a Jihar Gombe sun samu ne sakamakon tsare-tsare masu ma’ana, daidaiton hukumomi da kuma ba al’umma damar taka rawa a harkokin mulki.
A cewarsa, manyan ayyuka kamar shirin hanyoyi na Network 11-100 Roads Initiative, Muhammadu Buhari Industrial Park, Three Arms Zone, Agro-Livestock Development Zone, da kuma shirye-shiryen sabunta birane da ake ci gaba da aiwatarwa, sun nuna yadda dimokuraɗiyya ke iya inganta rayuwar jama’a.
“Gombe a yau ta zama abin koyi na abin da shugabanci mai hangen nesa, riƙon amana da kuma haɗa kan kowa zai iya cimmawa a ƙarƙashin tsarin dimokuraɗiyya,” in ji Gwamna Inuwa.
Yayin da ya amince da ƙalubalen tattalin arziki da na tsaro da ƙasar ke fuskanta, ya ce ci gaba da gudanar da mulkin dimokuraɗiyya da samun sauye-sauyen gwamnati cikin lumana babban ci gaba ne da ya cancanci a yi murna da shi.
Gwamnan ya kuma yaba wa masu fafutukar tabbatar da dimokuraɗiyya da hukumomi daban-daban, ciki har da ɓangaren shari’a, majalisun dokoki, kafafen yaɗa labarai da ƙungiyoyin farar hula, bisa sadaukarwa da gudummawar da suka bayar wajen karewa da ƙarfafa dimokuraɗiyyar Najeriya.
Haka kuma, ya buƙaci ‘yan Najeriya su ci gaba da kasancewa cikin haɗin kai tare da jajircewa wajen kare manufofin adalci, riƙon amana da shugabanci nagari.
Ya yi gargaɗi game da yaɗa labaran ƙarya da kuma kalaman da ke haddasa rarrabuwar kai, musamman yayin da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.
“Duk da ƙalubalen da ake fuskanta, dimokuraɗiyya ita ce ginshiƙin zaman lafiya, ba da damar shiga harkokin mulki, ci gaba da kuma bunƙasar ƙasa,” in ji shi.
A ƙarshe, Gwamna Inuwa Yahaya ya yi wa ɗaukacin ‘yan Najeriya fatan gudanar da bikin ranar dimokuraɗiyya cikin kwanciyar hankali, farin ciki da cikar buri.
