Tinubu ya yi alƙawarin mai da Abuja katafaren birni daidai da manyan birane na duniya

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Shugaba Bola Tinubu ya ce zai buƙasa Babban Birnin Tarayya (FCT) ta yadda zai zama babban birni mai yawan al’umma da tattalin arziki da ɗaga martabar ƙasa nan bakiɗaya.

Shugaba Tinubu, wanda mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya wakilta, ya bayyana hakan a ranar Laraba a Abuja yayin ƙaddamar da aikin Titin Arterial Road N5 (Obafemi Awolowo Way), daga mahaɗar Life Camp zuwa Ring Road III da ke yankin Dape.

Ya ce inganta hanyoyin sufuri a Abuja zai rage kuɗaɗen jigilar kayayyaki da ƙara jawo masu zuba jari tare da samar da guraben ayyukan yi ga al’umma.

A cewarsa, ingantattun ayyukan more rayuwa su ne ma’aunin da ke nuna yadda ƙasa take da ƙudurin ci gaba da kuma ƙarfin gwamnati wajen aiwatar da manufofinta.

“Babu wani babban birni da zai iya ɗaukar nauyin ƙasa idan aka ce manyan hanyoyi sun lalace sakamakon sakaci, uzurori da kuma ayyukan da aka bari ba a kammala ba,” ya faɗa.

Ya ƙara da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da saka hannun jari a manyan ayyukan raya ƙasa da za su inganta haɗin kai tsakanin yankuna, su ƙarfafa harkokin tattalin arziki tare da dawo da amincewar jama’a ga gwamnati.

“Ba za mu huta ba har sai mun mayar da Abuja ba kawai cibiyar gudanar da mulki ba, har ma babban birni da ya dace da martabar tarayyar Nijeriya,” in ji shugaban ƙasa.

Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin ta gaji ayyukan hanyoyi da ke buƙatar kulawa mai ɗorewa, amma ta tabbatar da ci gaba da gine-gine da gyaran hanyoyin ba tare da tangarɗa ba.

“Babu wani tsaiko ko ja da baya ko dakatar da aiki wajen ci gaba da ayyukan hanyoyin da muka gada. Hakan ne zai kawo ƙarshen al’adar barin ayyuka a tsakiyar hanya tare da dawo da imanin jama’a cewa gwamnati na iya kammala abin da ta fara,” ya faɗa.

Ya kuma bayyana cewa sashen aikin Arterial Road N5 da ke Dape gwamnatinsa ce ta tsara shi, ta samar da kuɗaɗensa kuma ta kammala shi, yana mai cewa hakan ya nuna an kauce wa tsohuwar al’adar da ke sa manyan ayyuka su riƙa zama cikin kasafin kuɗi na tsawon shekaru ba tare da kammalawa ba.

“A baya irin waɗannan ayyuka kan zama abin da ake ware wa kuɗi na tsawon shekara goma ko goma sha biyar tare da ba da uzuri ba. A wannan gwamnati, wannan zamani ya wuce,” in ji shi.

Shugaban ya yaba wa Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, bisa yadda yake jagorantar aiwatar da samar da ayyukan raya ababen more rayuwa a Abuja, tare da jinjina wa kamfanin da ya gudanar da aikin saboda cika alƙawarin da aka ɗora masa.

Ya ce sabon titin ba hanyar sufuri kaɗai ba ne, wata muhimmiyar hanya ce ya bunƙasa tattalin arziƙi da za ta sauƙaƙa zirga-zirga tare da rage asarar lokaci da cunkoson ababen hawa da ke haifar wa da mazauna yankin da ‘yan kasuwa tsaiko.

Tinubu ya bayyana cewa tsawon shekaru mahaɗar Life Camp ta kasance babbar matsalar cunkoso, amma kammala wannan hanya zai samar da haɗin kai tsakanin yankunan Dape, Karmo, Gwarinpa I, Kado, Idu da Mbora, tare da inganta hanyoyin shiga yankin masana’antu na Idu kamar yadda tsarin babban birnin tarayya yake.

Sai dai ya jaddada cewa ɗorewar irin waɗannan ayyuka na buƙatar haɗin kan gwamnati da al’umma. Don haka ya buƙaci mazauna yankin da ‘yan kasuwa su rika biyan haraji da kuɗaɗen filaye yadda ya kamata domin ƙarfafa gwamnatin Abuja wajen aiwatar da ƙarin ayyukan raya ƙasa.

Hakazalika, ya roƙi sarakuna da shugabannin al’umma da mazauna yankunan da su kare kadarorin gwamnati tare da hana lalata su.

By ukarofi