Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta ce ta ceto matafiya biyar da wasu da ake zargin ’yan bindiga ne suka yi garkuwa da su a kan hanyar Anka zuwa Bukkuyum.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, inda ya ce jami’an Sashen Yaki da Manyan Laifuka ne suka kai dauki cikin gaggawa bayan faruwar lamarin.
A cewarsa, lamarin ya faru ne da misalin karfe 7:00 na yammacin ranar 10 ga watan Yuni, lokacin da wasu dauke da makamai suka tare hanyar tare da yin garkuwa da matafiyan biyar.
Abubakar ya ce jami’an tsaro sun bi sawun wadanda ake zargin zuwa cikin daji, inda suka yi artabu da su ta hanyar musayar wuta.
Ya ƙara da cewa aikin ya yi nasarar kubutar da dukkan mutanen biyar ba tare da sun samu rauni ba.
Haka kuma, an kwato babura guda biyu da ake kyautata zaton maharan sun yi amfani da su wajen aikata laifin.
Rundunar ’yan sandan ta sake jaddada kudirinta na yaki da ayyukan ta’addanci da sauran laifuffuka a fadin jihar, tare da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ta kuma bukaci jama’a su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai ta hanyar samar da sahihan bayanai cikin lokaci domin taimakawa kokarin dakile aikata laifuka.
