Daga DAUDA USMAN a Legas
Rasuwar fitaccen ɗan kasuwa kuma jagoran al’ummar Arewa mazauna Jihar Legas, Alhaji Mohammed Dandamma Yabo, ta jefa al’umma cikin jimami da alhini.
Marigayin ya rasu ne a ranar Lahadin makon da ya gabata a mahaifarsa ta Jihar Sakkwato bayan fama da jinya. Kafin rasuwarsa, Alhaji Mohammed ɗandamma Yabo shi ne babban shugaban kasuwar sayar da doya ta Mile 12 da ke Legas. Haka kuma ya taɓa riƙe muƙamin shugaban ƙungiyar al’ummar Arewa (Northern Community) a Jihar Legas.
Marigayin, wanda ya rasu yana da shekaru 85 a duniya, ya bar mata biyu, ’ya’ya takwas, maza biyar da mata uku, tare da jikoki da dama. ɗaya daga cikin manyan ’ya’yansa, Auwalu Mohammed, na ci gaba da gudanar da harkokin kasuwancin doya a kasuwar Mile 12.
An yi wa marigayin jana’iza tare da binne shi bisa koyarwar addinin Musulunci. Al’umma da dama sun yi addu’ar Allah Ya jikansa, Ya gafarta masa kura-kuransa, tare da sanya shi cikin Aljannatul Firdausi.
Bayan cikar kwanaki bakwai da rasuwarsa, an gudanar da taron addu’o’in neman rahama gare shi ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar Shukura Yam Sellers Association tare da haɗin gwiwar babban shugaban kasuwar Mile 12 International Market, Alhaji Shehu Usman Jibrin Samfam.
Taron addu’ar ya samu halartar manyan sarakunan Hausawa mazauna Jihohin Legas da Ogun, shugabannin kasuwanni daban-daban, ’yan kasuwa da sauran jama’a daga sassa daban-daban.
Daga cikin manyan baƙin da suka halarci taron akwai Sarkin Fulanin Jihar Legas, Dakta Alhaji Mohammed Abubakar Bambado II, Galadiman Legas, Alhaji Aliyu Bambado, Marafan Legas, Alhaji Abdullahi Umar ɗan Asabe, da sauran sarakunan Hausawa daga Jihohin Legas da Ogun.
A jawabansu, makusantan marigayin da suka haɗa da sabon shugaban kasuwar na riƙon ƙwarya, Kwamared Ahmed D. Yusuf, da Alhaji Abdullahi Dan Filani Mai Doya, sun bayyana cewa marigayin ya kasance mutum mai kyawawan halaye da son jama’a.
Sun ce kafin rasuwarsa ya yi wasiyya ga waɗanda ya bari cewa duk wanda ya zo taron addu’arsa zai kasance yana ambaton kyawawan halayensa da ayyukan alheri da ya yi wa jama’a.
A cewarsu, wannan wasiyya ta nuna irin rayuwar nagarta da marigayin ya gudanar, inda suka buƙaci matasa da sauran al’umma su yi koyi da kyawawan halayensa.
Sauran waɗanda suka yi jawabi a wajen taron sun haɗa da Alhaji Shehu Usman Jibrin Samfam, Sarkin Fulanin Jihar Legas, Dakta Alhaji Mohammed Abubakar Bambado II, Alhaji Abdullahi Umar Dan Asabe, da Sanatan Legas ta Gabas, Mukhail Abiru.
Dukkansu sun yi addu’ar Allah Ya gafarta wa marigayin, Ya sa Aljanna ta zama makomarsa, tare da bai wa iyalansa, abokansa da al’ummar Legas baki ɗaya haƙurin jure wannan babban rashi.
Rasuwar Alhaji Mohammed Dan Damma Yabo ta bar babban giɓi a harkokin kasuwanci da shugabancin al’ummar Arewa a Legas, inda da dama suka bayyana cewa za a daɗe ana tuna gudummawar da ya bayar wajen haɗin kai, ci gaban kasuwanci da kyautata zamantakewar al’umma.
