Trump ya hana baƙi zuwa Amurka domin haihuwa kawai don samun zama ‘yan ƙasa ga ’ya’yansu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Gwamnatin Amurka ƙarƙashin jagorancin Shugaba Donald Trump ta ƙaddamar da wani sabon mataki na yaƙi da abin da ta kira “birth tourism”, wato tafiya zuwa Amurka da nufin haihuwa domin yaro ya samu zama ɗan ƙasar Amurka.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar a ranar Laraba, 10 ga Yuni, cewa ofisoshin jakadanci da na jakadun Amurka a ƙasashe daban-daban sun gano wasu tsare-tsaren da ake zargin suna taimaka wa baƙi samun bizar ziyara ta hanyar yaudara domin zuwa Amurka haihuwa.

A cewar ma’aikatar, waɗannan tsare-tsare sun haɗa da amfani da takardun bogi, masu taimaka wa neman biza ta haramtacciyar hanya da kuma horas da masu neman biza yadda za su kauce wa dokokin shige da fice.

Ma’aikatar ta jaddada cewa dokokin Amurka ba su amince da bayar da bizar ziyara ga mutum idan babban dalilinsa shi ne zuwa ƙasar domin haihuwa don yaron ya samu ɗan ƙasar Amurka.

“A ƙarƙashin Shugaba Trump, Ma’aikatar Harkokin Waje na kare martaba da sahihancin zama ɗan ƙasar Amurka ta hanyar kawo ƙarshen haramtattun shirye-shiryen haihuwa domin samun ɗan ƙasa. Ba a yarda wani baƙo ya samu bizar ziyara da nufin haihuwa a Amurka domin yaro ya samu ɗan ƙasar Amurka ba,” inji sanarwar.

Jami’an gwamnatin sun bayyana cewa wata ofishin jakadancin Amurka da ke yankin Yammacin Afirka ta gano tare da rusa wata ƙungiya da ta haɗa da fiye da mutum 100 da ake zargin sun yi amfani da takardun bogi da masu safarar biza domin samun damar shiga Amurka.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa an soke bizar wasu mutanen da ke da alaƙa da wannan shiri, yayin da ake ci gaba da aiki tare da hukumomin ƙasashen da abin ya shafa domin gano makamantan ayyukan.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce jami’an jakadanci na aiki tare da hukumomin tsaro tare da amfani da fasahar nazarin bayanai domin gano tafiye-tafiyen da ake zargi da kuma cibiyoyin da ke shirya irin waɗannan ayyuka.

Ta kuma yi gargadin cewa masu riƙe da biza da aka samu suna karya dokokin shige da fice na iya fuskantar soke bizarsu tare da hana su shiga Amurka nan gaba.

“Bizar Amurka gata ce, ba haƙƙi ba ne. Ma’aikatar Harkokin Waje na ɗaukar matakai a faɗin duniya domin dakile wannan cin zarafi, rusa cibiyoyin da ke shirya irin waɗannan tafiye-tafiye da kuma hukunta masu ƙoƙarin yaudarar tsarinmu,” inji gwamnatin Amurka.

Sabon matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Trump na tsaurara dokokin shige da fice da kuma hana amfani da tsarin zama ɗan ƙasar Amurka ta hanyar haihuwa a ƙasar domin samun wata fa’ida ta musamman.

By ukarofi