Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Aƙalla mutane huɗu ne suka rasa rayukansu yayin da wasu mutum 11 suka shiga hannun masu garkuwa da mutane bayan wasu ‘yan bindiga sun kai sabbin hare-hare a ƙananan hukumomin Kachia da Kajuru da ke Jihar Kaduna.
Rahotanni sun nuna cewa hare-haren sun faru ne tsakanin ranar Asabar zuwa Litinin a wasu ƙauyukan da ke yankin Kudancin Kaduna.
A ƙaramar Hukumar Kachia, maharan sun kai farmaki ƙauyukan Mafofadiya da Zagom Mazuga, inda suka kashe wani mazaunin yankin mai suna Joel Dauda.
Haka kuma, maharan sun yi awon gaba da mutane bakwai da suka haɗa da Leo Bakut, Kefas Hilary, Victoria Leo, Cristiana Joel, Iseal Joel, Hannatu Iseal da kuma Isreal James.
A wani hari daban da aka kai a ƙauyukan Kallah da Kufana na ƙaramar Hukumar Kajuru, an kashe wasu mutane biyu da aka bayyana sunayensu da Jagora Dabo da Misali Adamu.
Rahotanni sun kuma ce matar Jagora Dabo mai juna biyu tare da ‘ya’yanta na daga cikin mutanen da aka sace yayin harin.
Mazauna yankin sun kuma tabbatar da cewa an kashe wani mutum a ƙauyen Kufana, sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto ba a bayyana sunansa ba.
Sabbin hare-haren sun sake tayar da hankalin al’ummomin Kudancin Kaduna, inda mazauna yankin ke nuna damuwa kan yadda hare-haren kashe-kashe da sace-sace ke ci gaba da faruwa a yankunan karkara.
Wasu mazauna yankin sun yi kira ga jami’an tsaro da gwamnati da su ƙara ƙaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da kamo waɗanda ke da hannu a irin waɗannan hare-hare.
Lamarin ya kuma sake janyo muhawara kan tasirin matakan sulhu, sasanci da shirye-shiryen gyaran hali da gwamnati ke aiwatarwa domin jawo masu aikata laifuka su ajiye makamansu.
Mazauna yankunan da abin ya shafa sun bayyana cewa har yanzu suna rayuwa cikin fargaba sakamakon yawaitar hare-haren ‘yan bindiga, garkuwa da mutane da kuma kashe-kashe a yankin.
