Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Sabbin bayanai sun fito a ranar Laraba a shari’ar da ake yi wa tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama da Raya Sararin Samaniya, Hadi Sirika, inda Hukumar EFCC ta shaida wa Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya da ke Abuja cewa jirgin da aka ƙaddamar a matsayin Nigeria Air a watan Mayun 2023, jirgi ne da aka haya daga Ethiopian Airlines na tsawon kwanaki uku domin baje koli.
Rahoton News Point Nigeria ya nuna cewa, a cewar EFCC, an kawo jirgin Najeriya ne kwanaki kaɗan kafin ƙarshen gwamnatin tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, sannan aka gabatar da shi ga jama’a a matsayin hujjar cewa an samu nasarar kafa kamfanin jirgin saman ƙasa na Nigeria Air da aka daɗe ana jira.
EFCC ta yi zargin cewa jirgin ya isa Abuja a ranar 27 ga Mayu, 2023, ya kasance a filin jirgin sama tare da tambarin Nigeria Air na ƙasa da awanni 72, sannan aka mayar da shi Habasha a ranar 29 ga Mayu, 2023, ranar da Sirika ya bar ofis.
An bayyana waɗannan zarge-zargen ne ta bakin shaida ta 12 na masu gabatar da ƙara, Christopher Odofin, jami’in bincike na EFCC, yayin da yake bayar da shaida a gaban Mai Shari’a S.C. Oriji a ci gaba da shari’ar Sirika da wasu mutum uku kan zargin amfani da mukami ba daidai ba da kuma karkatar da kuɗaɗen gwamnati da suka haura Naira biliyan 2.
Sirika na fuskantar shari’a tare da ‘yarsa Fatima Sirika, surukinsa Hamma Sule, da kamfanin Al Buraƙ Global Investment Limited, kan gyararren tuhuma mai ƙunshe da laifuka shida.
A cewar wata sanarwa da kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya fitar, Odofin ya shaida wa kotun cewa takardun da aka samu daga Ethiopian Airlines sun nuna cewa jirgin da aka nuna a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja a ranar 27 ga Mayu, 2023, an haye shi ne musamman domin bikin ƙaddamar da shi da tambarin Nigeria Air.
Yayin da yake karanta yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Ethiopian Airlines da masu shirya Nigeria Air, shaidar ta bayyana cewa jirgin ya tashi daga Addis Ababa a daren 26 ga Mayu, 2023, ya isa Abuja a ranar 27 ga Mayu domin bikin ƙaddamarwa, sannan ya koma Habasha a ranar 29 ga Mayu.
A cewar shaidar, yarjejeniyar ta fayyace manufar hayar da kuma tsawon lokacin da jirgin zai yi a Najeriya.
“Jirgin zai tashi daga Addis Ababa a daren 26 ga Mayu, 2023 domin isa Filin Jirgin Sama na Abuja da safiyar 27 ga Mayu. Jirgin zai kasance a filin jirgin Abuja domin baje kolin tambarin Nigeria Air har zuwa ranar 28 ga Mayu, 2023. Zai tashi daga Abuja da safiyar 29 ga Mayu, 2023. Ma’aikatan jirgin za su kasance na Ethiopian Airlines kuma za su sanya kayan aikinsu na hukuma.
“Gwamnatin Tarayyar Najeriya da Nigeria Air za su iya samar da wasu mutane sanye da kayan Nigeria Air domin ɗaukar hotunan bikin ƙaddamarwa. Haka kuma za a iya kai su Addis Ababa domin su dawo tare da jirgin zuwa Abuja,” inji wani sashe na yarjejeniyar.
Odofin ya shaida wa kotun cewa lokacin da aka shirya ƙaddamar da jirgin ba haɗari ba ne, domin an tsara shi ne ya yi daidai da ranar ƙarshen wa’adin Sirika a ofis, wato 29 ga Mayu, 2023.
Ya kuma yi zargin cewa an gabatar da jirgin ga ‘yan Najeriya a matsayin hujjar cewa aikin Nigeria Air ya zama gaskiya, alhali yarjejeniyar ta kasance ta ɗan lokaci ne kawai.
A cewarsa, bayan an kammala bajekolin jirgin, an cire tambarin Nigeria Air daga jikinsa kafin a mayar da shi Addis Ababa.
Jami’in binciken ya ce takardun da Ethiopian Airlines ta bayar sun nuna cewa yarjejeniyar hayar ta shafi kwanaki uku ne kawai, daga 27 zuwa 29 ga Mayu, 2023.
Ya ƙara da cewa kamfanin jirgin ya bayyana hakan ne a cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 12 ga Yuni, 2023, da ya aike wa EFCC domin amsa tambayoyi kan aikin Nigeria Air.
Odofin ya kuma shaida wa kotun cewa duk da cewa an ƙirƙiri Nigeria Air a matsayin kamfanin jirgin saman ƙasa, yarjejeniyar hayar da Ethiopian Airlines an kulla ta ne a ranar 24 ga Mayu, 2023, kwanaki biyar kacal kafin Sirika ya sauka daga mukami, kuma manufarta ita ce sanya tambarin Nigeria Air a jikin jirgin.
Shaidar ta kuma yi bayani kan wata kwangilar ba da shawara da aka bai wa kamfanin Tianaero Nigeria Limited domin kafa Nigeria Air, wanda ya ce yana da alaƙa da wani mutum mai suna Gabriel Tilmann, wanda ya bayyana a matsayin na kusa da Sirika.
A cewarsa, an fara bai wa kamfanin kwangilar da ta haura Naira miliyan 299 a ranar 4 ga Afrilu, 2022.
Ya ce daga baya an ƙara wa kwangilar kuɗi a ranar 17 ga Oktoba, 2022, inda darajarta ta kai sama da Naira miliyan 599.
Jami’in EFCC ya yi zargin cewa an ƙara wa kwangilar kuɗin ne bisa umarnin Sirika saboda kusancinsa da mamallakin kamfanin.
“Tawagar bincike ta cimma wannan matsaya ne bayan nazarin wayar Enitan Muyiwa Abel, wanda shi ne Sakataren Dindindin a ma’aikatar Sirika. An gano wani saƙon murya da aka aika masa yayin da Sirika yake Spain, inda aka umarce shi da ya tabbatar an bai wa Tianaero Nigeria Limited kwangilar,” inji shi.
A yayin shari’ar, masu gabatar da ƙara sun miƙa wasu takardu ga kotu, ciki har da faifan sauti da ake zargin ya ƙunshi saƙon muryar Sirika.
Kotun ta amince da karɓar faifan da takardun da ke tare da shi a matsayin hujja, tare da yi musu rajista a matsayin Eɗhibit 37.
Lauyan masu gabatar da ƙara ya nemi a kunna faifan a zaman kotu na gaba.
Babu ɗaya daga cikin lauyoyin masu kare waɗanda ake tuhuma da ya yi adawa da karɓar takardun.
Daga nan ne kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa wani lokaci domin ci gaba da shari’ar da kuma sauraron faifan sautin, yayin da EFCC ke ci gaba da gabatar da hujjoji kan zarge-zargen da ake yi wa tsohon ministan da sauran waɗanda ake tuhuma dangane da aikin Nigeria Air.
