Kyari da Ma’aji sun musanta zargin kashe tiriliyan 210 a NNPC

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD da SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Babban Darakta kuma Shugaban Kamfanin Man Fetur na ƙasa na Nijeriya (NNPCL), Mele Kyari, ya bayyana matakin da Kwamitin Majalisar Dattawa kan Binciken Asusun Gwamnati ya ɗauka na bayar da umarnin cafke shi a matsayin abin mamaki matuƙa, yana mai cewa bai taɓa karɓar wata gayyata daga kwamitin ba kafin a fitar da wannan umarni.

A wata wasiƙa da ya aike wa Shugaban Kwamitin bayan sanar da umarnin cafke shi a ranar 10 ga Yuni, 2026, Kyari ya ce tun da farko ya sanar da kwamitin cewa yana ƙasar waje domin karɓar magani, don haka ba zai iya halartar zaman binciken ba a wannan lokaci.

Ya bayyana cewa a wasiƙar da ya rubuta tun ranar 11 ga Mayu, 2026, ya sanar da kwamitin halin da yake ciki tare da nuna shirinsa na amsa gayyatar da zarar ya dawo Nijeriya.

“Na kuma bayyana cewa ina shirye in amsa gayyatar kwamitin nan da nan bayan dawowata gida,” inji Kyari.

Tsohon shugaban NNPCL ya jaddada cewa bai yi watsi da gayyatar Majalisar Dattawa da gangan ba, yana mai cewa bai samu ko ganin wata sabuwar takardar gayyata ba kafin a fitar da umarnin cafke shi.

“Cikin girmamawa nake sanar da ku cewa ban karɓi ko gani ba wannan gayyata da ake magana a kanta. Da ace ta riske ni, da na amsa ta cikin gaggawa,” inji shi.

Kyari ya kuma bayyana cewa yanayin lafiyarsa a halin yanzu ba ya ba shi damar bayyana a gaban kwamitin, inda ya buƙaci a riƙa tuntuɓar lauyoyinsa idan akwai wasu tambayoyi ko bayanan gaggawa da ake buƙata yayin da yake ci gaba da jinya a ƙasashen waje.

Ya tabbatar wa kwamitin cewa zai ba da cikakken haɗin kai wajen gudanar da binciken, kuma zai bayyana da kansa a gaban ‘yan majalisar da zarar lafiyarsa ta inganta.

Da yake kare yadda ya tafiyar da harkokin NNPCL lokacin da yake jagoranci, Kyari ya ce tawagar da ya jagoranta ta sauya kamfanin daga cibiyar da ke fama da asara zuwa kamfani mai cin riba da gudanar da harkokinsa bisa tsarin kasuwanci.

Ya kuma ce duk mu’amalolin da aka gudanar a zamaninsa an rubuta su tare da adana bayanansu yadda ya kamata, kuma suna nan a buɗe domin duba su idan buƙatar hakan ta taso.

“Har yanzu ina godiya ga ƙasata bisa damar da ta ba ni na yin hidima cikin gaskiya da jajircewa,” inji shi.

Tun da farko dai Kwamitin Majalisar Dattawa kan Binciken Asusun Gwamnati ya bayar da umarnin cafke Kyari bayan ya kasa bayyana a gabansa a wani zama da aka shirya. Kwamitin na gudanar da bincike ne kan bayanan kuɗi da mu’amalolin NNPCL, ciki har da wasu bayanan kuɗi da suka haura naira tiriliyan 210 da ake dubawa. Sanata Victor Umeh ne ya gabatar da ƙudirin neman a bayar da umarnin cafke Kyari, yayin da Sanata Adams Oshiomhole ya mara masa baya.

Duk da wannan ci gaba, Kyari ya dage cewa ba shi da abin da yake ɓoyewa, yana mai cewa zai ci gaba da ba Majalisar Dattawa cikakken haɗin kai domin gano gaskiyar batutuwan da suka shafi kuɗaɗen NNPCL.

Shi ma tsohon Babban Jami’in Kuɗi (CFO) na NNPCL, Umar Ajiya Isa, ya yi watsi da wannan zargi, yana mai cewa, adadin Naira tiriliyan 210 da ake magana akai ya fi yawan kuɗin shiga da kamfanin ya samu a tsawon lokacin.

Kwamitin Majalisar Dattawa kan Asusun Gwamnati ne ya bayar da umarnin kama Kyari a ranar Laraba bayan ya kasa halartar zaman binciken da aka shirya kan wannan batu. Sanatoci Saliu Mustapha (Kwara ta Tsakiya) da Tony Nwoye (Anambra ta Arewa) sun buƙaci a ba Kyari wata dama saboda yana ƙasar Jamus domin karɓar magani.

Sai dai wasu mambobin kwamitin sun yi adawa da hakan, suna kira da a bayar da sammacin kama shi. Sanata Abdul Ningi (Bauchi ta Tsakiya) ya ce ba za a amince da uzurin rashin lafiya ta baki kawai ba sai an gabatar da hujjojin asibiti. Haka kuma Sanata Victor Umeh (Anambra ta Tsakiya) ya gabatar daƙudurin neman a bayar da sammacin kama Kyari.

Mataimakin shugaban kwamitin, Sanata Peter Nwaebonyi (Ebonyi ta Arewa), ya goyi bayan ƙudurin, yana mai cewa: “Wannan shi ne karo na tara da kwamitin ke zama kan tambayoyi 19 da Ofishin Babban Mai Binciken Kuɗi na Tarayya ya gabatar kan NNPCL. Lokaci ya yi da za a bayar da umarnin kama Mele Kyari domin mu kammala aikinmu.”

Bayan an kaɗa ƙuri’ar murya, shugaban kwamitin, Sanata Ibrahim ɗankwambo, ya bayyana cewa: “Duk inda Mele Kyari yake, a kamo shi a kawo shi gaban wannan kwamitin.”

Da yake gabatar da bayaninsa a gaban kwamitin, Umar Ajiya ya ce zargin cewa Naira tiriliyan 210 ta ɓace ba gaskiya ba ne. Ya ce: “Idan da gaske an rasa irin wannan maƙudan kuɗaɗe a lokacin da muke jagoranci, da ba za mu iya fitar da rahoton binciken kuɗi (audited accounts) ba.”

Ya ƙara da cewa: “A cikin lokacin da ake magana a kai, jimillar kuɗin shiga na NNPCL kusan Naira tiriliyan 54.5 ne. Ta yaya za a ce Naira tiriliyan 210 ta ɓace alhali kuɗin da aka samu bai kai haka ba?”

Ajiya ya kuma musanta rahoton cewa an kashe Naira biliyan 5.8 wajen rijistar sabon kamfanin NNPCL Limited. Ya ce adadin da aka biya ya kamata a tantance shi daga Hukumar CAC da Hukumar Haraji ta ƙasa.

A cewarsa: “Rahotannin da ba su da tushe suna bata sunan mutane, kamfani da kuma Nijeriya baki ɗaya. Hukumomin ƙasa da ƙasa suna amfani da irin waɗannan bayanai wajen tantance tattalin arzikin ƙasa.” Ya ƙara da cewa ya kamata a tambayi masu zargin: “Idan har Naira tiriliyan 210 ta bace, to ina ta shiga?”

Ya buƙaci hukumomi kamar EFCC da NFIU su gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin. A ƙarshe, kwamitin ya umurci Umar Ajiya da tsohon Babban Jami’in Zuba Jari na ɓangaren Haƙar Mai na NNPCL, Bala Wunti, su sake bayyana a gabansa cikin makonni biyu domin ci gaba da bincike.

By ukarofi