Mahajjata mata biyu daga Sakkwato sun rasu bayan kammala aikin hajjin 2026

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Mahajjata mata biyu daga Jihar Sakkwato sun rasu a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya bayan sun kammala gudanar da ibadar aikin hajjin shekarar nan ta 2026.

Mataimakin Amirul Hajji na jihar kuma Babban Alƙalin Alƙalan Jihar, Alhaji Sodangi Acida, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da Shugaban Sashen Yaɗa Labarai da Sadarwa na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Sokoto, Malam Faruku Umar, ya fitar.

Mahajjatan da suka rasun sun haɗa da Malam Ladi Umar daga ƙaramar Hukumar Bodinga da kuma Malam Hadiza Umar daga ƙaramar Hukumar Yabo.

Alhaji Sodangi Acida ya bayyana cewa wasu mahajjata mata biyu da suka samu raunuka a wannan hatsari suna ci gaba da karɓar magani a wani asibiti a Saudiyya.

Ya ce, ɗaya daga cikinsu tana jinya ne sakamakon karayar ƙashi, yayin da ɗayar kuma take karɓar magani saboda karkacewar ƙashi a hannu.

Mataimakin Amirul Hajjin ya isar da saƙon ta’aziyyar Gwamnatin Jihar Sokoto ga iyalan mamatan, tare da addu’ar Allah Ya gafarta musu kura-kuransu, Ya kuma saka su da Aljannatul Firdaus.

Haka kuma, ya sanar da cewa rukunin farko na alhazan Jihar Sokoto zai fara komawa Nijeriya daga Saudiyya a ranar 14 ga watan Yuni.

A cewarsa, za a gudanar da jigilar dawowar alhazan ne bisa tsarin “wanda ya fara zuwa, shi zai fara komawa,” domin tabbatar da tsari da adalci wajen dawo da mahajjatan gida.

Ya kuma yi kira ga alhazan da su bi ƙa’idojin da aka gindaya kan kayan da za su ɗauka yayin dawowa gida.

Ya jaddada cewa nauyin kayan kowane mahajjaci bai kamata ya wuce kilogram 32 ba, domin gujewa matsaloli a filayen jiragen sama.

A wani ɓangare kuma, Babban Sakataren Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Sokoto, Alhaji Ibrahim Umar JJ, ya yaba wa Gwamna Ahmad Aliyu bisa irin goyon bayan da ya bai wa alhazan jihar tun daga farkon tafiyar Hajji har zuwa kammalawarta.

Ya kuma yabawa mambobin tawagar jihar, shugabannin hukumar, ma’aikatanta da kuma alhazan bisa haɗin kai da goyon bayan da suka bayar, wanda ya taimaka wajen gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026 cikin nasara.

By ukarofi