Atiku shi ne mafitar ƙasar nan — Hajiya Humaira Kano

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

An bayyana ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar ADC, Alhaji Atiku Abubakar (Turakin Adamawa), a matsayin wanda kaɗai zai iya fitar da Nijeriya daga halin da take ciki a yanzu.

Shugabar matan jam’iyyar ADC a Jihar Kano kuma shugabar ƙungiyar Atiku Network Initiatives, Hajiya Aisha Ibrahim Hassan, wadda aka fi sani da Humairan Kano, ce ta bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a taron gangamin haɗin kan ‘yan jam’iyyar ADC da ta shirya, wanda aka gudanar a ɗakin taro na Gidauniyar Kano a ranar Asabar da ta gabata.

Ta ce ta shirya taron ne domin haɗa kan ‘yan jam’iyyar ADC tare da nuna cikakken goyon baya ga takarar Wazirin Adamawa. A cewarta, Atiku Abubakar shi ne kaɗai mafita ga matsalolin da ƙasar ke fuskanta, musamman na rashin tsaro, inda ta bayyana shi a matsayin mutum nagari mai kishin ƙasa da burin inganta rayuwar al’umma.

Hajiya Humaira Kano ta ce da zarar ɗan takarar nasu ya lashe zaɓe mai zuwa, za a kawo ƙarshen rashin tsaron da ake fama da shi tsawon shekaru. Ta ƙara da cewa Atiku ya san irin ƙalubalen da ƙasar ke ciki, don haka ba zai bari a ci gaba da wahalar da ‘yan ƙasa ba.

Ta kuma yi kira ga ‘yan jam’iyyar ADC da sauran al’ummar ƙasa da su zaɓi cancanta a lokacin zaɓe domin ci gaban Nijeriya, tana mai cewa ƙasar na da albarkatu masu yawa da bai kamata ‘yan ƙasa su ci gaba da rayuwa cikin wahala da rashin tsaro ba.

A nasa jawabin bayan taron, shugaban matasa na jam’iyyar ADC na ƙasa kuma ɗan takarar kujerar Majalisar Dattawa a yankin Kano ta Tsakiya, Hon. Balarabe Ahmed Rufa’i, ya ce jam’iyyar ADC ita kaɗai ce ta rage wa ‘yan Nijeriya wadda idan ta samu nasara za ta kawo ƙarshen wahalhalun da ake ciki.

Ya ce al’umma na cikin mawuyacin hali, inda mutane ke barin garuruwa saboda rashin tsaro, wasu kuma ba sa iya ciyar da iyalansu, yayin da manoma ke kasa zuwa gonakinsu, abin da ya jefa ƙasar cikin ƙarancin abinci.

Shugaban matasan ya jaddada cewa idan suka samu nasara a zaɓe mai zuwa, za su kawo sauye-sauye ta hanyar dokoki da tsare-tsare da za su rage wa jama’a wahala, tare da inganta rayuwa da samar da damammakin dogaro da kai ga mata da matasa.

Shi ma, Muhammad Usman Mado, Sarkin Yakin Wazirin Adamawa Atiku Abubakar, ya ce Nijeriya a yanzu ba ta da jagora da ya fi Atiku, inda ya ce takararsa ba don neman kuɗi ba ce, sai don kishin talakawa da damuwar da suke ciki.

Ya ce ‘yan kasuwa sun durƙushe, wasu al’umma sun bar garuruwansu sakamakon rashin tsaro, yayin da wasu yankuna ke fama da matsalar rayuwa mai tsanani.

Mado ya kuma yi zargin cewa wasu ‘yan jam’iyya na amfani da mukamansu wajen gurgunta tafiyar jam’iyyar tun daga matakin ƙananan hukumomi zuwa jihohi da ƙasa baki ɗaya, inda ya yi kira ga magoya baya da su haɗa kai domin tabbatar da nasarar jam’iyyar.

A jawabin godiya da aka gabatar a madadin ɗan takarar, Alhaji Atiku Abubakar, mai ba shi shawara kan wayar da kan al’umma game da muhimmancin katin zaɓe, Kwamared Idris Unguwar Gini, tare da takwaransa na kafafen sadarwa na Hausa, Alhaji Sharfadi Katin Kwari, sun gode wa waɗanda suka shirya taron, tare da nuna jin daɗinsu kan yadda aka karɓi takarar Atiku Abubakar da girmamawa daga jama’a da ‘yan jam’iyya.

By ukarofi

Leave a Reply