
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane da su miƙa wuya ko kuma su fuskanci ƙarfin gwamnati akan miyagun laifukan da suka aikatawa wauen cutar da al’umma a sassan Nijeriya.
Rahotanni sun bayyana cewa, Tinubu ya bayyana hakan ne acikin saƙonsa na Ranar Dimukraɗiyya ta 12 ga watan Yunin 2026.
Ya ce, Gwamnatin Tarayya ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ta’addanci, inda ta lalata wani babban sansanin ISWAP a yankin Arege da ke Jihar Borno.
Ya ƙara da cewa, yawan mutanen da ake kashewa sakamakon ta’addanci ya ragu da kashi 81 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar 2015, yayin da aka kawar da sama da ’yan ta’adda 13,000 a cikin shekarar ta gabata.
Tinubu ya kuma bayyana cewa sama da mutane 124,000 daga cikin mayaƙa da iyalansu sun ajiye makamansu ta hanyar shirin Atisayen Safe Corridor tun daga shekarar 2023 zuea yanzu.
Haka kuma Shugaban ƙasar ya gargaɗi masu cigaba da aikata laifuka da cewa damar miƙa wuya ba za ta kasance a bude ba har abada.
Don haka ya buƙaci da su ajiye makamai tare da miƙa kansu ga hukumomin tsaro domin taimaka wa aikin ƙoƙarin dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a sassan ƙasar.
