Hanyoyin Gwamnatin Tarayya a Katsina sun yi mummunar lalacewa – Kwamred Suleiman

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina

Shugaban ƙungiyar cigaban Funtua Kwamred Mannir Suleiman ya koka a kan yadda hanyoyi mallakar gwamnatin tarayya su kayi mummunar lalacewa a jihar katsina.

A hira da yayi da manema labarai a katsina Kwamred Suleiman ya ce idan har gwamnatin tarayya ba ta kammala wasu aikin hanyoyi a jihar ba ta zirga zirga tsakanin jihar katsina da makwabtan ta zai tsaya cik.

Ya bada misali da hanyar Katsina zuwa Kano da Gidan Mutum Ɗaya zuwa Katsina da aka bada aikin hanyar a shekarun baya amma har ya zuwa yanzu babu wani bayani game da cigaban aikin hanyar musamman hanyar Katsina zuwa Kano.

” Ya za ayi a kammala aikin hanyar Kano zuwa kan Iyakar Kano zuwa Katsina amma daga nan aikin ya tsaya,”Inji Kwamred Suleiman.

Shugaban ƙungiyar ya bayyana cewa masu ababen hawa idan sun tashi bin hanyar Gidan Mutum Ɗaya zuwa Funtua da Gidan Mutum Ɗaya zuwa Katsina sun shiga cikin zullumi da fargaba.

Ya ce itama hanyar Katsina zuwa Mararrabar Ƙankara an fara aikin gyaran hanyar amma aikin ya tsaya ba tare da wani bayani kan dalilin tsaida aikin ba.

“Saboda haka ina kira da babbar murya ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta fara aikin gyaran hanyoyin da ke faɗin jihar domin bunƙasa kasuwanci da huɗdoɗin yau da kullum” Mannir ya ce.

Ya buƙaci Gwamna Dikko Raɗɗa da ministoci da manyan jami’an gwamnatin tarayya da yan majalisar ƙasa da su saka baki a lamarin domin a cigaba da aikin gyaran hanyoyin kafin faɗuwar damina sosai a jihar.

Ya yaba wa gwamna Dikko Raɗɗa kan gina tare da faɗaɗa hanyoyi a musamma a mayan biranan jihar da ya bayyana a matsayin tamkar faɗaɗa zumunci da kasuwanci a jihar.

Kwamred Suleiman ya bada misali da yankin Funtua inda ya fito inda ya ce malam duk ya gina mayan hanyoyi da faɗaɗa wasu wanda hakan yasa garin Funtua ta ƙara bunƙasa ta harkar kasuwanci da zamantakewa.

By ukarofi

Leave a Reply