‘Yan sanda sun harbi ɗan gwagwarmaya, Sowore yayin zanga-zanga a Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

An garzaya da ɗan fafutukar ‘yan ɗan-adam kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore zuwa asibiti bayan ya faɗi sakamakon arangama tsakanin ‘yan sanda da masu zanga-zanga.

Al’amarin ya faru ne a yankin Unity Foundation da ke Birnin Tarayya Abuja, ranar Juma’a.

Masu zanga-zangar sun yi cincirindo ne don nuna adawarsu halin da rashin tsaro, matsin tattali da abin da ya suka kira da “shugabanci mara kyau” da al’ummar Nijeriya ke fuskanta.

A cewar jaridar Vanguard, shaidu sun ce zanga-zangar, wadda ta haɗa ‘yan gwagwarmaya da ƙungiyoyin al’umma, ta samu tsaiko ne a lokacin da jami’an tsaro suka watsa hayaƙi mai sa hawaye domin tarwatsa jama’a, lamarin da ya sa mutane da dama watsewa domin neman sauƙi game da al’amarin.

Haka nan shi ma Sowore al’amarin ya shafe shi, amma daga bisani ya dawo cikin hayyacinsa, inda bayan haka ne aka garzaya da shi zuwa wani asibiti domin duba lafiyarsa.

Tuni dai masu zanga-zangar suka ta yin alla-wadai da matakin ‘yan sandan akan abin da suka kira da neman ɗaukar matakin gaggawa akan matsalolin da ƙasar ke ciki.

By Babaji

Leave a Reply