Trump ya janye sabon yunƙurin Amurka na kai wa Iran hari

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Donald Trump na Amurka ya sanar da soke hare-haren da aka shirya kai wa Iran bayan Tehran ta yi barazanar cewa za ta ƙara tsananta yaƙin idan aka cigaba da sabon yaƙin.

Trump ya ce, an samu cigaba a tattaunawar da ake yi, saboda haka an dakatar da hare-haren da aka tsara, duk da cewa takunkumin ruwan teku kan Iran zai ci gaba da aiki.

Sai dai jami’an Iran sun yi gargadin cewa duk wani sabon hari daga Amurka zai fuskanci martani mafi tsauri, kuma hakan na iya ƙara faɗaɗa rikicin a yankin.

Wannan wani babban sauyi ne daga matakin Trump na farko na ɗaukar babban matakin soja akan Iran matuƙar ta rushe tattaunawar da ke gudana tsakanin ɓangarorin biyu.

Shugaban Amurkan a wata sanarwa ya ce ya ɗauki matakin ne sakamakon shawarwari daga masu ruwa da tsaki na shiyya da kuma ƙasashen Gabas ta Tsakiya.

By Babaji

Leave a Reply