Ranar Dimokuraɗiyya: Gwamna Raɗɗa ya yaba wa jajurtattun dimokuraɗiyya

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya taya al’ummar Jihar Katsina da ɗaukacin ‘yan Najeriya murnar cika shekaru 27 da ranar dimokuraɗiyya ta ƙasa.

Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa ranar 12 ga Yuni rana ce mai muhimmanci da ke nuna ƙudurin al’ummar Najeriya na zaɓar ‘yanci, adalci da mulkin dimokuraɗiyya fiye da komai.

Ya ce ranar tana tunatar da mu irin sadaukarwar da aka yi domin Najeriya ta tsaya a kan ginshiƙin dimokuraɗiyya da take morewa a yau.

Gwamnan ya yi gagarumar karramawa ga fitattun ‘ya’yan Jihar Katsina waɗanda gudummawar da suka bayar a tafiyar dimokuraɗiyyar Najeriya ba za ta taɓa mantuwa ba. Ya karrama marigayi Janar Shehu Musa Yar’adua, wanda jajircewarsa da sadaukarwarsa wajen ci gaban ƙasa suka taimaka wajen shimfiɗa hanyar komawar Najeriya ga mulkin dimokuraɗiyya.

Haka kuma ya tuna da marigayi tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, cikin girmamawa, bisa rayuwarsa da ya sadaukar wajen yi wa Najeriya hidima a matsayin shugaban soja da kuma shugaban farar hula, yana tsayawa tsayin daka wajen kare haɗin kan ƙasa da bin doka da oda.

A lokaci guda, Gwamna Raɗɗa ya yaba da kyakkyawan tarihin marigayi shugaban ƙasa Alhaji Umaru Musa Yar’adua, wanda duk da gajeren wa’adin mulkinsa, ya yi fice wajen mutunta kundin tsarin mulki da kuma nuna ƙauna ta gaskiya ga al’ummar Najeriya.

Gwamnan ya ce:

“Jihar Katsina tana alfahari da waɗannan manyan ‘yan Najeriya. Ba jiharsu kaɗai suka yi wa hidima ba, sun sadaukar da kansu gaba ɗaya ga ƙasar da suka yi imani da ita. “Sadaukarwarsu tana tunatar da mu ma’anar shugabanci na gari, kuma muna ɗaukar tarihin rayuwarsu a matsayin jagora.”Inji Dikko

Gwamna Raɗɗa ya kuma yi amfani da wannan dama wajen yaba wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa jajircewarsa na tsawon lokaci wajen kare dimokuraɗiyya a Najeriya. Tun kafin ya zama shugaban ƙasa, Tinubu na daga cikin fitattun masu gwagwarmayar kare dimokuraɗiyya, kuma yana daga cikin waɗanda suka taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da muhimmancin ranar 12 ga Yuni a tarihin Najeriya.

Ya jaddada cewa dagewar Shugaba Tinubu wajen kare ‘yancin jama’a, ba wa al’umma damar shiga harkokin mulki, da kuma tabbatar da bin doka da oda tsawon shekaru, ya taka muhimmiyar rawa a ci gaban dimokuraɗiyyar Najeriya.

Gwamna Raɗɗa ya kuma yi kira ga dukkan ‘yan Najeriya da su yi nazari a kan ma’anar wannan rana tare da sabunta ƙudurinsu na rungumar ƙimomin dimokuraɗiyya kamar ɗaukar alhaki, adalci da kare haƙƙin kowane ɗan ƙasa. Ya kuma buƙaci al’ummar Katsina su ci gaba da mara wa kyakkyawan mulki, zaman lafiya da ƙoƙarin ci gaban da gwamnatinsa ke yi baya.

“Dimokuraɗiyya ba tsarin mulki kaɗai ba ne, alƙawari ne da muke yi wa junanmu a matsayin al’umma. A wannan rana, mu sabunta wannan alƙawari tare da haɗa kai wajen gina Katsina da Nijeriya da kowane ɗan ƙasa zai yi alfahari da su.”Raɗɗa ya ce.

Gwamna Raɗɗa ya sake taya al’ummar Katsina da dukkan ‘yan Nijeriya murnar zagayowar ranar dimokuraɗiyya, tare da addu’ar Allah ya ci gaba da ba ƙasar nan zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba.

By ukarofi

Leave a Reply