
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ministan Tsaron Birtaniya, John Healey ya yi murabus, bayan ya zargi Firaministan ƙasar, Keir Starmer da gazawa wajen cika alƙawuran inganta kuɗaɗen da ake kashewa a aikin soji.
A wasiƙarsa ta Murabus, Mista Healey, ya ce Keir Starmer da ma’aikatar kuɗi ba su fitar da kuɗaɗen da ake buƙata wajen bada tsaron ƙasa, lamarin ya sa ya shiga damuwa akan ƙaruwar barazanar tsaro daga Rasha.
A cewar wakilin BBC, ya ga wasiƙun murabus da dama a rayuwarsa amma bai taɓa ganin mafi ban mamaki kamar ta Healey ba.
Shirin inganta tsaron ƙasa na Birtaniya na tafiyar hawainiya, inda ma’aikatar tsaro da ta kuɗaɗen da suka gagara cimma matsaya akan yada za’a samu kuɗaɗen bunƙasa tsaron ƙasa da aikin soji.
A wani labarin kuwa, Keir Starmer, ya naɗa Dan Jarvis a matsayin sabon Sakataren Tsaro na ƙasar, bayan murabus ɗin Healey daga muƙamin.
Wannan naɗi na zuwa ne a daidai locacin da harkokin tsaro da siyasar ƙasar ke fuskantar muhimman sauye-sauye, yayin da ake sa ran sabon sakataren zai jagoranci manufofin tsaron Birtaniya a matakai na gaba.
