Gyaran tsarin shari’a: NBA Gombe ta fara makon lauyoyi da addu’o’i na musamman

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe

Ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA), reshen Jihar Gombe, ta fara gudanar da makon lauyoyi na shekarar 2026 da addu’o’in na musamman, inda ta buƙaci a ƙara inganta tsarin shari’a domin tabbatar da cewa adalci ya isa ga kowane ɗan Najeriya ba tare da nuna bambanci ba.

An fara shirye-shiryen makon ne da addu’ar Musulmi da aka gudanar a masallacin Juma’a na Modibbo Bubayero da ke Gombe, inda lauyoyi, alƙalai da sauran masu ruwa da tsaki suka hallara domin neman taimako da shiriyar Allah wajen samun nasarar shirye-shiryen da aka tanada.

Da yake jawabi bayan addu’ar, Shugaban NBA reshen Gombe, Barrista Alhassan Mu’azu, ya bayyana cewa babban abin da Makon Lauyoyi na bana zai mayar da hankali a kai shi ne hanyoyin gyara da ƙarfafa ɓangaren shari’a domin ya yi wa kowa aiki cikin adalci.

Ya ce akwai buƙatar a tabbatar da cewa tsarin shari’ar Najeriya yana kare haƙƙin kowane ɗan ƙasa, ba tare da la’akari da matsayinsa na kuɗi ko ilimi ba.

“Muna son tsarin shari’a da zai yi wa kowa aiki; mai arziki da talaka, mai ilimi da marar ilimi, ba tare da wariya ko nuna bambanci ba. Adalci haƙƙi ne na kowane ɗan kasa,” in ji shi.

Mu’azu ya ƙara da cewa saƙonnin da aka gabatar a wajen addu’ar sun tunatar da lauyoyi muhimmancin kare mutuncin sana’arsu tare da gudanar da aikinsu bisa gaskiya da ƙwarewa.

A huɗubarsa, mataimakin babban limamin masallacin Modibbo Bubayero, Barrista Ali Hammari, ya yi kira ga lauyoyi da su kasance masu tsoron Allah, riƙon amana da bin ƙa’idojin sana’arsu.

Ya bayyana cewa sana’ar lauya an assasa ta ne domin tabbatar da gaskiya da adalci, amma ya nuna damuwa kan yadda wasu ke amfani da ita wajen neman abin duniya kawai ba tare da tunawa da hisabin lahira ba.

Ya ce duk amanar da aka ɗora wa lauya za a tambaye shi a kanta a gaban Allah, don haka wajibi ne su gudanar da aikinsu cikin gaskiya da kyawawan ɗabi’u.

Barrista Hammari ya kuma yi addu’ar Allah ya ba da nasarar gudanar da dukkan shirye-shiryen makon lauyoyin cikin zaman lafiya, haɗin kai da albarka.

Ita ma shugabar kwamitin shirya makon lauyoyi na 2026, Barrista Hannatu Dauda Simon, ta ce fara makon da addu’o’i na nuna muhimmancin neman taimakon Ubangiji da kuma haɗin kan masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da adalci a al’umma.

Ta bayyana cewa taron zai haɗa lauyoyi da masana daga jihohin Arewa maso Gabas domin tattauna muhimman gyare-gyaren da ake buƙata a ɓangaren shari’a, tare da duba rawar da lauyoyi za su taka wajen kare haƙƙokin jama’a da bunƙasa ci gaban ƙasa.

Ta ce taken makon lauyoyi na shekarar 2026 shi ne:”Ƙarfafa Adalci Ta Hanyar Gyare-Gyare: Lauyoyi a Matsayin Jakadun Sauyi.”

A cewarta, taken ya nuna irin muhimmiyar rawar da ake sa ran lauyoyi za su taka wajen kawo sauye-sauyen da za su inganta tsarin shari’a da tabbatar da adalci a Najeriya.

By ukarofi

Leave a Reply